Babu alamar yaɗuwar korona – NCDC

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Hukumar da ke yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC) ta kwantar da hankalin jama’a bayan tabbatar da samun sabon mutum da ya kamu da cutar korona a jihar Kuros Ribas, inda ta ce babu wata alamar yaɗuwar cutar a yanzu.

A wata sanarwa da Darakta Janar na hukumar, Jide Idris, ya fitar, ya bayyana cewa ana sa ido kan dukkan mutanen da suka yi hulɗa da wanda ya kamu da cutar, kuma komai na tafiya yadda ya kamata.

Gwamnatin jihar Kuros Ribas ta tabbatar da ɓullar cutar ne a ranar Talata, bayan shekaru da hukumar lafiya ta duniya ta ayyana cewa an kawo ƙarshen matakin gaggawa na annobar a duniya. Kwamishinan lafiya na jihar, Henry Ayuk, ya ce wanda aka fara samu da cutar ɗan ƙasar China ne da ke aiki a ƙaramar hukumar Akamkpa, wanda ya shigo Najeriya a ranar 17 ga Maris kafin daga bisani ya fara nuna alamun cutar.

NCDC ta ce an killace marar lafiyan tare da kula da shi bisa ƙa’idojin lafiya, kuma yana samun sauƙi. Hukumar tare da abokan hulɗarta da ma’aikatar lafiya ta jihar sun ƙaddamar da matakan daƙile yaɗuwar cutar, ciki har da bibiyar waɗanda suka yi hulɗa da marar lafiyan da kuma ƙarfafa sa ido. Haka kuma, an shawarci ‘yan Najeriya da su ci gaba da kiyaye tsafta kamar wanke hannu akai-akai da bin ƙa’idojin kariya, tare da gaggauta neman kulawar likita idan sun ji ba su da lafiya.

By ukarofi