
A yau Laraba Kotun Ƙoli a ta sanar da ɗage yin hukunci akan ƙarar da David Mark, shugaban tsagin jam’iyyar ADC ya shigar akan Nafiu Bala, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa.
Mai Shari’a Lawal Garba, wanda ke jagorantar kwamitin alƙalai guda biyar, ya bayyana hakan ne bayan lauyoyin bangarorin biyu sun gabatar da hujjojinsu a gaban kotu.
Ya bayyana cewa, za a sanar da ranar da za a yanke hukuncin daga baya ga dukkan ɓangarorin da ke shari’ar.
Mark ya roƙi kotun da ta dakatar da aiwatar da hukuncin Kotun Daukaka Kara na ranar 12 ga watan Maris, wanda ya yi watsi da ƙarar sa a kan rikicin shugabanci a jam’iyyar.
Tun da fari, Kotun Ɗaukaka Ƙara mai alƙalai uku, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Uchechukwu Onyemenam, ta tabbatar da ƙin amincewa da ƙarar Mark, inda ta ce ƙarar bata da inganci kuma ba ta dogara da batutuwan da kotun farko ta yanke ba.
David Mark ya ɗaukaka ƙara ne kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja na ranar 4 ga watan Satumba, 2025, wanda ya ƙi amincewa da wasu bukatun hana aiwatarwa da Nafiu Bala ya gabatar.
Rikicin shugabanci da ke cikin ADC ya bar jam’iyyar ba tare da shugabanci na ƙasa da aka amince da shi ba, kamar yadda INEC ta bayyana.
