Gwamnatin Tarayya ta ci tarar Kamfanin Meta Platforms dala miliyan 220 bayan bincike ya nuna cewa kamfanin na raba bayanai a dandalin ta na Facebook da WhatsApp ta hanyar da ya saɓa wa dokar kariyar bayanan jama’a ta Nijeriya.
Dokta Adamu Abdullahi, muƙaddashin babban jami’in hukumar FCCPC ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a.
Ya ce kamfanin na Meta ya ware bayanan yan Nijeriya a kan dandalin ta ba tare da izininsu ba, ya yi amfani da su wajen kasuwanci da kuma nuna wariya da nuna bambanci ga ‘yan Nijeriya wanda abun ba haka yake ba a wasu ƙasashe.
Kamfanin na Meta bai ce komai ba, amma FCCPC a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce kamfanin ya samar da wasu takardu a lokacin da suka gana da hukumar.
Shugaban FCCPC, Abdullahi ya ce an gudanar da binciken ne tare da Hukumar Kare bayanai ta Najeriya kuma an shafe sama da watanni 38 ana gudanar da wannan binciken.
