
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja a ranar Laraba zuwa ƙasar Birtaniya don fara hutunsa na shekara wanda zai ɗauki tsawon mako biyu.
Zai yi amfani da lokacin ne don hutun aiki da kuma yin nazari ga ayyukan gwamnatinsa na gyare-gyaren harkokin tattali, kamar yadda mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da tsare-tsare, Mista Bayo Onanuga ya faɗa cikin wata sanarwa a Abuja.
Bayan hutun ya ƙare ne shugaban zai dawo Nijeriya.
