Gwamnan Zamfara ya yi bikin cikar shekaru 28 da ƙirƙiro jihar, ya buƙaci a yi addu’ar samun Zama lafiya

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya buƙaci a ƙara kaimi wajen addu’o’in zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya a daidai lokacin da ƙasar ke bikin cika shekaru 64 da samun ƴancin kai.

Jihar Zamfara na cikin jihohi shida da gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha ta kafa a ranar 1 ga Oktoba, 1996.

Gwamna Lawal, acikin wani saƙon fatan alheri da kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar Talata, ya ce ranar 1 ga watan Oktoba rana ce ta musamman ta yin tunani akan irin gwagwarmaya da sadaukarwar da kakannin da suka yi fafutukar tabbatar da ƴancin Nijeriya, haɗin-kai da wadata suka yi.

Sanarwar ta cigaba da cewa, “Gwamna Dauda yayi kira da a yi tunani a hankali game da halin da jihar Zamfara ke ciki, da kuma faɗin jihar, wanda ya daɗe yana fama da ƙalubalen da ba a taba ganin irinsa ba na rashin tsaro da ɓangaren lafiya da ilimi da matsalar abinci da lalata ababen more rayuwa”.

“A yau mun samu damar yin tunani a kan abin da mu a matsayinmu na gwamnati ke yi don canza alƙibilar jiharmu yayin da a cikin shekara guda na gwamnatin mu, jihar ta samu gagarumin sauyi kuma tana kan hanyar ci-gaba da ikon Allah.”

“Muna samun ci-gaba sosai a fannin tsaro, noma da samar da abinci, kiwon lafiya, fannin ilimi, samar da ababen more rayuwa, da sake fasalin ayyukan gwamnati da dai sauransu”.

“Duk wadannan ana samun su ne duk da karancin albarkatun da jihar ke samu. Manyan abubuwan da aka samu na wasu nasarorin sun yi daidai da ajandar cetonmu ya zuwa yanzu.”

“A fannin tsaro, mun kafa, horarwa, da kuma samar da kayan aiki ga Community Protection Guards (CPGs). Mun kafa Asusun Tsaro (STF), muna ba da tallafin kuɗi/taimako na wata-wata don cigaba da kokarin hukumomin tsaro na yau da kullun, tare da kawar da bangar siyasa.”

“A bangaren ilimi, mun kafa dokar ta-ɓaci a fannin ta hanyar biyan kuɗaɗen jarabawar WAEC da NECO, wanda ya kai adadin Naira biliyan 3.4, da wasu makarantu da aka sake ginawa, gyarawa, da kuma samar da kayan aiki a makarantun firamare, sakandare da manyan makarantu a faɗin ƙananan hukumomi 14 na jihar, da kuma daidaita kuɗaɗen takwarorinsu don sauƙaƙe cikakken damar samun tallafin da ake buƙata daga abokan haɗin-gwiwa.

“Har’ilayau, gwamnatina ta kafa dokar ta-ɓaci a fannin kiwon lafiya, da ɓullo da shirye-shiryen wayar da kan jama’a kyauta tare da samar da muhimman magunguna ga marasa galihu, da gyara da samar da cibiyoyin kiwon lafiya a jihar da sake farfaɗo da samar da kiwon lafiya.”

“Don bunƙasa noma a Zamfara, gwamnatina ta samar da takin zamani da sauran kayan amfanin gona don noman damina da na rani, mun gyara da inganta Kwalejin Noma da Fasaha ta Bakura.

“Domin jin daɗin ma’aikata, mun daidaita albashi, fensho, ga ma’aikatan gwamnati da waɗanda suka yi ritaya; mun samu nasarar daidaita ma’aikatun sassan da Hukumomi (MDAs) don inganta aikin gwamnati tare da aiwatar da mafi karancin albashi na N30,000.00 ga ma’aikatan gwamnati a faɗin jihar da ƙananan hukumomi goma sha hudu; gaggauta biyan albashi da fansho ga ma’aikatan gwamnati da waɗanda suka yi ritaya a kowane wata; Samar da fakitin jin-daɗi kamar na kashe-kashe, da kuma alawus na wata goma sha uku da Sallah”, inji gwamnan.

By Babaji