Gwamnatin Katsina ta wajabta yin gwajin ƙwayoyin halitta kafin aure

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta wajabta yin gwaje gwajen ƙwayoyin halitta ga waɗanda ke shirin yin aure ciki harda gwajin cutar sikila.

Gwamnan jihar Dikko Raɗɗa, ya bayyana cewa ya zama wajibi ga masu shirin yin aure a jihar su yi gwajin cutar sikila domin daƙile yaɗuwar cutar.

Raɗɗa ya bayyana haka ne a ranar Litinin a jawabin da ya gabatar wajen buɗe cibiyar kula da cutar sikila da kuma ƙaddamar da rabon magungunan cutar kyauta ga masu ciwon na sikila duk wata a babban asibitin jihar dake birnin Katsina.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN ya rawaito cewa, magungunan da gwamnati ta raba sun haɗa da na sikila da kuma maganin zazzaɓin cizon sauro.

An shirya shirin ne ta hanyar gidauniyar uwargidan gwamnan dake tallafa wa al’uma wato SASHIN, tare da haɗin gwiwar ma’aikatar lafiya ta jihar.

A cewar gwamnan, gwamnatin jihar ta samar da dokar da ta haramta aure ba tare da an yi wa waɗanda ke shirin yin aure gwaje gwajen ba.

Gwamnan ya kuma ce, an kafa dokar ne don ganin an hana auratayya tsakanin masu ɗauke da sinadarin ƙwayoyin jini na AS don kare lafiyar kowane daga cikin ma’auratan.

Raɗɗa ya ci gaba da cewa, idan har aka bar irin wannan aure, ma’auratan da ‘ya’yansu da iyaye da gwamnati da kuma sauran jama’a za su iya faɗawa cikin wahala.

Don haka ne ya buƙaci iyaye da su tabbatar an yi wa ’ya’yansu gwajin kafin su yi aure don tabbatar da cewa dukkaninsu basa ɗauke da ƙwayar halittar AS wadda ke saurin yaɗa cutar a tsakanin al’umma.

By ukarofi