Da kaji biyu na fara kiwo har na kai 150 – Zainab Aqeela

“Soshiyal midiya kwalba ce, idan ka so ka zuba giya ko lemu”

Daga UMAR GARBA, a Katsina

Zainab Lawal Abdulƙadir wadda aka fi sani da Aqeela, matashiya ce kuma ‘yar kasuwa, bayan nan ta kan gabatar da shirye-shiryen faɗakarwa, nishaɗantarwa gami da ilmintarwa a kafafen sada zumunta na zamani wato ‘Social media’. Ta yi fice a tsakanin matasa maza da mata bawai a Jihar Katsina ba kaɗai har da sauran jihohin arewacin Nijeriya. Wakilin Manhaja a Katsina ya tattauna da Zainab Aqeela akan batutuwan da suka shafi kasuwancinta, alaƙarta da matasa da kuma yadda ta ke gabatar da shirye-shiryen da suka shafi matasa maza da mata a kafafen sada zumunta na zamani. Mai karatu zai ji burin da wannan matashiya da kuma irin faɗi-tashin da ta yi na ganin kasuwancinta ya tsaya da ƙafafunsa. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

MANHAJA: Za mu so jin taƙaitaccen tarihinki?
ZAINAB: Assalamu alaikum warahmatullah. Da farko dai sunana Zainab Lawal Abdulƙadir, an haife ni a garin Katsina cikin wata unguwa da ake kira Galadunchi, sai dai na taso a unguwar Tsohuwar Kasuwa a nan cikin birnin Katsina. Na yi makarantar firamare a Gobarau ‘Primary School’, na kuma yi karatun sakandare a makarantar ‘Government Day Secondary School’ Dutsin ‘Safe Low Cost’, yanzu kuma ina ci gaba da karatun gaba da sakandare a Kwalejin da ake kira Sir Usman Nagogo College of Arabic and Islamic studies. wannan dai shine a taƙaice.

An fi sanin ki a harkar Kasuwanci. Mece ce sana’arki?
Gaskiya ne ni ‘yar kasuwa ce a halin yanzu, na kan sayar da abubuwa da dama, amma dai yanzu na fi maida hankali akan yin dambun naman kaji da farfesun kaji da dai sauran dukkan kasuwancin da ya jivinci nama, sai dai na fi sayar wa masu sari na kan kuma karɓi kwangilar yi wa masu hidimar bikin suna ko aure ko masu hidimar wani babban taro

Yaushe kika fara wannan kasuwancin?
Na fara wannan kasuwancin tun cikin shekara ta 2019, duk da cewa a baya na yi sana’o’i  daban daban na bari, amma a halin yanzu wannan sana’ar ta sayar da dambun naman kaji ita ce na ke yi.

Ya kike ɗaukar sana’a ga ‘ya mace?
A duk lokacin da aka yi mani wannan tambayar na kan faɗawa mata cewar, sana’a abu ce mai matuƙar muhimmanci, saboda haka sana’a a waje na tana da matuƙar muhimmanci, akwai rufin asiri a ciki don haka ban rabe ba ga mace mai aure ko marar aure, idan mu ka ɗauki muhimmancin sana’a ga mace wacce ba ta yi aure ba za ka ga ko da iyayenta suna ba ta ci su ba ta sha su yi mata sauran buƙatun yau da kullum, akwai abinda ita kanta za ta buƙata wanda idan tana sana’a ba sai ta jira iyayenta ko wani ya ba ta ba, kawai za ta ɗauka ta yi hidimarta saboda babu mai iya jure yawan bani bani sai Allah.  Muhimmancin sana’a kuma ga matar aure shi ne, za ta iya taimakon mai gidanta ta wajen yiwa yara wata hidimar kamar kuɗin makarantar boko ko ta Islamiyya da dai sauran ƙananan buƙatun yau da kullum wanda ba sai ta jira mijinta ya bata ba. Haka nan ta ɓangaren zamantakewa idan kina sana’a za ki iya taimakon mijinki wajen siyen wasu abubuwan ba sai kin tsaya jiran sa ba, yin haka kin taimake shi don haka sana’a ga ‘ya mace tana da matuƙar muhimmanci.

Waɗanne jihohi ne sana’arki ke kaiwa?
Gaskiya alhamdulillah, sana’ar nan tana kaiwa jihohi da yawa cikin ƙasar nan, tun daga Arewa har zuwa Kudu, baya ga nan gida Katsina akwai wasu jihohin  kamar irin su Kano, Kaduna, Bauchi, Gombe, Abuja, Kalaba, Lagos da dai sauran su saboda bazan iya tuna sauran jihohin ba a halin yanzu.

Waɗanne sana’o’i ne suka fi dacewa da mata?
Sana’o’in da su ka fi dacewa da mata ko kuma waɗanda mata za su iya yi gaskiya suna da yawa, ya dangata da irin kasuwanci ko sana’ar da mace ta zaɓa da kanta don ta fara. 

Wane mataki kike da burin takawa a wannan kasuwanci da kike yi?
Gaskiya ina da buri da dama, amma babban buri na shine, na buɗe ko na mallaki katafaren wurin cin abinci wato ‘Restaurant’ irin na zamani wanda duk lokacin da wani ko wata ya/ta je wajen ya samu dambun nama da ma  dukkan nau’in abinci da yake buƙata. Misali ban fiye yin farfesun kaji ba na ajiye saboda kada ya lalace sai idan na samu waɗanda ke son ayi masu saboda abu ne da ke da ruwa-ruwa, idan aka ajiye shi za ya iya lalacewa, to amma idan na mallaki babban ‘Restaurant’ za ni kuma tanadi wajen ajiye shi ta yadda ba za ya yi saurin lalacewa ba. Bayan wannan ina da burin zama ‘yar jarida, shiyasa ma na ke bibiyar kafafen yaɗa labarai, koda yake dama na kan gabatar da shirye-shiryen da su ka shafi matasa a kafafen sada zumunta wato soshiyal midiya.

A ganinki ta ya ‘yan’uwa mata za su samu jarin fara sana’a?
Wato idan ana maganar jarin fara sana’a na kan ƙarfafa wa mata gwiwa cewar, ka da su ce sai sun samu jari mai yawa kamar dubu 50 ko 100 sa’annan su fara sana’a. Misali ni kaina a lokacin da na fara sana’a ban fara da babban jari ba, abinda na fara da shi bai fi dubu biyar ba, saboda na fara daga siyan kaji biyu ne, akwai wata rana wanda ya fara kawo mini kaji da ya zo ya ga yadda na cika robobi da kaji ya yi mamaki sosai saboda yasan cewar duka-duka na fara da kaji biyu ne, amma yanzu gashi ya same ni kasuwa ta havvaka daga kajin dubu biyar zuwa na dubu 150, wani lokacin ma har na dubu 200 na kan yi dambun naman su a rana. Idan zan iya tunawa kafin wannan lokacin, akwai lokacin da na daina sana’ar saboda kasan yadda sana’ar mata ta ke, wani lokacin sai a cinye rabin jarin, amma daga baya sai wani aminina ya bani tallafi don na ci gaba. Wata rana ina gida zaune sai ga shi ya kawo mani kifin da bai fi na dubu ɗaya ba da nufin na soya na ci, amma sai na ƙi ci, sai kawai na soya shi na kuma yi amfani da Soshiyal midiya na gaya wa masu siyayya wurina cewar na dawo da sana’a fa, saboda a lokacin har dambun kifi dama na kan soya na sayar daga haka jarina ya dawo ya ci gaba da havvaka har zuwa inda ake yanzu.

Ko kin tava samun tallafin da gwamnatoci ke cewa suna ba wa masu ƙanana da matsakaitan sana’o’i?
Eh gaskiya na tava samu, gwamnatin Jihar Katsina ta tava bani tallafi. Akwai wata ƙungiyarmu mai suna ‘Katsina state Talent and Interpreneurship’ a ƙarƙashin wannan ƙungiyar mun taɓa kaiwa gwamnan Jihar Katsina ziyara a matsayin ƙananan ‘yan kasuwa, sai dai an yi rashin sa’a lokacin da mu ka ziyarci gwamnan babu wanda ya je da sana’ar da za ta nuna cewar mu ‘yan kasuwa ne, amma da taimakon Allah kamar na san gwamnan za ya nemi sanin sana’armu sai na tafi da sauran dambun naman kaji na Naira dubu 18,500 bayan an gabatar da mu gare shi sai mai girma gwamna ya ce to shi an ce ma shi mu ‘yan kasuwa ne amma bai ga ko ɗaya daga cikin mu da ta zo da sana’ar ta ba. Bayan an gabatar da ni a matsayin mai sana’ar dambun nama, sai gwamnan ya ce mini ina dambun naman kajin. Take sai na ce ranka ya daɗe ga shi nan sai ya karɓa har ma sai da ya ci sa’annan aka raba wa sauran ‘yan majalisarsa da ke wajen to a nan ne aka ba ni tallafin.

Ki kan gabatar da shirye-shirye na matasa a kafafen sadarwa na zamani. Shin me ye alfanun waɗannan shirye-shiryen?
Haka ne. Na kan gabatar da shirye-shiryen da suka shafi matasa. Wasu shirye-shiryen na ƙarfafa wa matasa ne akan su nemi sana’a, wasu kuma na neman ilimi, wasu kuma na nishaɗantarwa ne. Mu kan shirya waɗannan shirye-shiryen don mu faɗakar ko mu nishaɗantar ko kuma mu ilimintar da matasa, kuma alhamdulillah shirye-shiryen suna yin tasiri akan su saboda suna amfani da abin da mu ke ƙoƙarin nuna masu don cigabanmu bakiɗaya.

Kasancewar ki mai amfani da Soshiyal midiya, a ganinki matasa suna amfani da ita ta hanyar da ta dace?
Ita Soshiyal midiya kamar kwalba ta ke, idan ka so sai ka zuba giya a ciki, idan kuma kaso sai ka zuba lemu ciki ka sha. Wasu suna amfani da ita don tallata hajarsu kamar mu, wasu don sada zumunci, wasu don nishaɗi, wasu kuma suna amfani da ita bisa ra’ayinsu. Duk yadda ka yi amfani da ita haka ka so. Wanda ya ke amfani da ita ta hanyar da ba ta dace ba shi a ganin sa hakan ne ya dace a wajen shi saboda yana ganin wayarsa ce kuma datarsa ce.  Amma dai ya kamata mu matasa mu dinga amfani da wannan kafar sadarwa ta hanyar da ta dace; kamar tallata kasuwancin mu, sada zumunta, neman ilimi da sauran abubuwan da mu ka san za ya amfane mu. Hakazalika zan so in yi amfani da wannan damar in ja kunnen matasa kan mayar da kafafen soshiyal midiya dandalin yaɗa jita-jita, ko labarai da ka iya tada fitina a tsakanin al’umma.

Masu bibiyarki a shafukan sada zumunta su kan ce hijabi yana maki kyau?
Alhamdu lillah. Ka san duk abin da ya zama bin umarnin Allah yana kyau, sai dai idan ka ɗauki huɗubar sheɗan. Saka hijabi abu ne mai kyau ga ‘ya mace kuma kamar yadda aka yi umarnin tsayar da Salla a cikin Al’ƙurani, haka aka umarce mu da saka hijabi. 

Wacce tambaya masu bibiyarki a shafukan sada zumunta suka fi yi maki?
Da yawa sukan tambaye ni yaushe za ki yi aure. A nan ne na ke son al’umma su san cewar shi fa aure lokaci ne, ko mace ko namiji kowa yana jiran lokacin aurensa ne. Don haka babu wanda ya isa ya jawo lokacin idan bai zo ba, haka nan idan lokacin ya yi kuma to babu wanda ya isa ya ture lokacin. Ya kamata jama’a su fahimci cewar komai lokaci ne, wata rana sai dai aji wani ya zo ya ɗauke mu.

Wane irin miji kike da burin aure?
Ina da burin auren namiji mai addini wanda za ya dinga ɗora ni akan hanyar da ta dace, mutafannini wato wanda ta kowanne ɓangare yana da sani, mai ilimin boko da na addini. Kuma na fi son namijin da tsawon mu ya zo ɗaya, ba na son wanda na fi shi tsawo.

Wane kalar kaya kika fi son ki saka?
Duk da na taso cikin al’ummar Hausawa, a gaskiya ina da ra’ayin son qananan kaya kamar riga da wando, ko riga da siket, ko kuma dogon wando, amma saboda na taso cikin al’ummar Hausawa a yanzu na fi son na saka ɗinkin atamfa ko doguwar riga.

Wacce shawara za ki ba wa ‘yan’uwa mata akan su tashi su kama sana’a?
Shawara ta a nan su gaggauta neman sana’a saboda kamar yadda na faɗa ma ka a baya, sana’ar mace tana da matuƙar muhimmanci ko don ki wuce raini a tsakanin ƙawaye ko kuma ga wasu mazan. Saboda za ka ji wasu suna faɗar cewa ta dameni da; tura mani kati, tura mani data da dai sauransu. Don haka ko don ta kaucewa waɗannan ƙananan maganganun ta tashi ta kama sana’a. Idan kina sana’a za ki ji ki a natse, ɗan anko ko kuma ki ga wata ƙawarki ta siyi abu na yayi saboda mu mata mu na da son ƙyale-ƙyale kin ga kin huta da jefa kanki wani hali kamar na damuwa ko bin wata hanyar da ba ta kamata ba. Sana’a ta na da muhimmanci. Mata mu tashi mu nemi sana’a.

Wane abu ne ke ɓata ma ki rai?
A halin yanzu gaskiya babu abin da ke ɓata mini rai kamar na kasa sana’ata, ban siyar ba, shine kawai abin da ke vata min rai. Saboda idan mutane su ka san abinda ke ɓata ma ka rai to kuwa za su dinga tsokanarka da shi don haka damuwa ta na kasa sana’ata ban siyar ba shi ne rai na za ya ɓaci.

Me ke saurin faranta ma ki rai?
Abin da ke faranta mani rai yanzu shi ne, mutane su yi ta odar kasuwancina. Na ji ana cewa ina da babban taro ko zan yi baƙi za ki mun farfesun kaji ko ina son dambun naman kaji na dubu kaza. Na yi ta jin ‘alert’ ya na shigowa wayata.

Wane ƙalubale kike fuskanta a harkar kasuwancinki?
Ƙalubalen da ni ke fuskanta bai wuce na ‘yan bashi ba, wani lokacin mutane sukan karɓi bashi kuma ga shi kana jin kunyar mutum, wasu kuma za su karɓa sai su nuna ma ka yanzu za su bayar da kuɗin, amma su ƙi bayarwa, daga baya abin ya zama bashi. Su kuma su kan manta cewar, ni ba bashi ake ba ni ba idan zan siyo kayan a kasuwa. Duk abin da zan siya sai na bada kuɗin, idan ma na karɓi bashi ina biya a kan lokaci. 

Waɗanne nasarori kika samu kawo yanzu?
Alhahamdulillah, gaskiya na samu nasarori da dama ta hanyar kasuwancin nan. Wannan hirar da kake yi da ni nasara ce. Baya ga jaridar Blueprint Manhaja, na yi hira da ‘yan jarida irin su DW Hausa da sauran kafafen yaɗa labarai shima nasara ce. Bayan nan ina yin abubuwan buƙatun rayuwa da kaina ba sai na jira an yi mani ba. Da sana’ar nan ina taimakon ɗan’uwa da ‘ya’yan dangi. Wannan duk nasara ce. Uwa-uba za ka ga abu ka na so, ba tare da tunanin ya za ka yi ba, ka cire ka siya, ba wanda ya jika, kuma ba inda ka yi ƙaramar murya. Waɗannan kaɗan kenan daga cikin nasarorin da na samu ta sanadiyyar sana’a.

Mun gode da lokacinki da kika ba mu.
Ni ma na gode sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *