Assalamu alaikum ya ‘yan uwa na matasa, ina mai maku barka da war haka. A ɗan tsakanin nan batun kirki ya ja hankalin mutane da dama. Kuma wani ɓangare ne na kalaman manyan malamai.
Kasancewa jajirtacce na nufin kasasncewa mutum mai kirki, zama mutum mai kirki ba gazawa ko tsoro ba ne. Ba kuma gazawa ba ce don kana taimakon wasu, abin da nake nufi shi ne ka zamo mai kirki ga kowa, don hakan ne mafi dacewa, yana da matuƙar muhimmanci ka kyautata wa waɗanda kake tare da su da ba su girma.
Ina ganin kamar tsarin da muke tafiyar da rayuwarmu a halin yanzu bai dace ba, ina nufin a nan gida Nijeriya da sauran sassan duniya, abin da muke gani na ƙara rura wutar rashin zaman lafiya tsakanin al’umma kama daga masu bambancin siyasa da addini.
Ya kamata mu san cewa, kirki yana taimakawa wajen gudanar jini, da rage hawan jini, yana inganta rayuwar mutane su yi tsawon rai da rayuwa mai inganci. Abin ban sha’awar shi ne kirki baya yawa ko kaɗan, babbar illar shi ne a ce babu baki ɗaya kuma a kyauta ake samnunsa ba tare da an biya wani abu ba.
Na taɓa jin an yi bincike kan halayyar Zomo a shekarun 1970. Wani ɓangare an samu kyakkyawan sakamako, wani kuma akasin hakan, shi ya sa na ke son sanin dalilin hakan. Bincikena ya gano min zomon ya kasance cikin kwanciyar hankali sakamakon kulawar da wani mai bincike ya ba shi.
Na kaɗu matuƙa a matsayina na injiniyan sinadarai (Chemical Engineer), jikina ya ba ni akwai wani saƙon gaggawa da ba a isar ba, wannan abun kuwa ba komai ba ne sai kirki, taimako da zai inganta rayuwarsu.
A ƙarshe zan lissafo abubuwan huɗu na samun ingantaccen rayuwa;
– Ka riƙa sauraren abin da mutane ke faɗa, ta haka za ka samu sauƙin fahimtar abin da ake nufi maimakon ka yanke hukunci kai tsaye.
– A duk lokacin da aka yi maka magana cikin fushi, ka yi ƙoƙarin tausasa harshenka idan za ka ba da amsa, ka sassauta muryarka cikin nishaɗi ka tambaye shi/ta abin da ke damunsa.
– A koda yaushe ka yi ƙoƙarin janyo mutanen da lamari ya shafa, idan kana yin haka zai nuna kana ba su daraja. Mutane ba sa jin daɗi idan ba a nuna musu ƙauna ko kulawa ba.
– ɗaukar mataki. Ka tabbatar ka fahimci yanayin da ake ciki idan wani abu ya faru na rashin kyautatawa ba lallai sai ya shafe ka kai tsaye ba, idan an fusata ka yi ƙoƙarin nutsuwa don kar ka ɗauki matakin da bai dace ba.
Daga MUSTAPHA MUSA MUHAMMAD. 08168716583.
