KILAF AWARD 2024: Finafinai 510 suka shiga gasa

DAGA MUKHTAR YAKUBU

Aƙalla finafinai ɗari biyar da goma ne suka samu shiga gasar bajekolin finafinai ta KILAF AWARD ta wannan shekarar wadda shi ne taro karo na bakwai da za a gudanar tun farkon fara taron a shekara ta 2018.

Daraktan shirya taron KILAF AWARD, Muhammad Galadima ne ya sanar da hakan a lokacin tattaunawarsa da wakilinmu a kan shirye shiryen bikin na wannan shekarar. 

Muhammad Galadima ya ce, “A bana sai dai mu ƙara godiya ga Allah a game da wannan gasar. Saboda ka ga wannan shi ne karo na bakwai da za a yi. Kuma a shekarar da ta gabata mun samu finafinai guda 50 daga ƙasashe 21 da suka shiga gasar. Amma a bana wani abin mamaki a wannan shekarar kafin mu kai ga rufe karɓar finafinan a ƙarshen watan Agustan da ya gabata, mun samu finafinai da suka shiga gasar har guda 510 daga ƙasashe 54, don haka wannan abin alfahari ne ga wannan gasar da kullum abin yake ƙara haɓaka.

Kuma wani abu da zai ƙara ba ka mamaki a bana shi ne, hukumar gudanarwa ta Jami’ar Bayero ta bayar da dama ga duk wani ɗalibi da ya shirya fim da ya dace, ta ajiye kuɗi dubu ɗari biyar za a bayar ga duk ɗalibin da ya shirya fim da ya dace a gasar a duk inda yake a duniya. To ga wannan wani abu ne da ba a saba yi ba. Don haka a yanzu tsare tsaren wannan biki ya yi nisa, za a bayar da dama masu ɗaukar nauyi su shigo sosai da sosai. Kuma a wannan shekarar kusan za a gabatar da kashi saba’in na abubuwan da za a gudanar a cikin Jami’ar Bayero. Kamar kowacce shekara akwai yawon buɗe Idanu ga baƙi da za su zo. Sai cin abinci da sarakuna kamar yadda aka saba yi a otal ɗin Tahir, da sauran abubuwa, yayin da kuma a wannan shekarar muna sa ran za a yi bikin bada kyautuka a babban ɗakin taro na Gidan Gwamnatin Kano domin a samu damar shigowa a tsakanin gwamnati da mutane.

To kuma abin da zai ba ka sha’awa ga wannan taron shi ne yana taimaka wa tattalin arzikin Jihar Kano, saboda idan baƙi suka shigo, dole sai sun sayi abubuwan da a ke sayarwa a Kano da hawa mota wanda hakan zai taimaka wa ci gaban tattalin arzikin Jihar Kano da kuma samun kuɗin shigar ta. Don haka ya kamata ace wannan abin wani abu ne ba wai Kannywood kawai ba, kamata ya yi a ce duk wani wanda yake kishin Hausa da Hausawa ya bayar da gudunmawa a duk inda yake a duniya, saboda magana ake ta assasa harsunan Afirika. 

To duk wanda ya yi fim a Afirika, ko da wanne yare ya yi shi, in dai na Afirika ne, ko da a wata ƙasa yake a cikin Turai, in dai fim ɗin da yaren Afirika ya yi, to KILAF ta na yi masa maraba.

Don haka a yanzu, mun turo finafinan ga alƙalan gasar suna can suna ailki ba dare ba rana, don ganin an samu sakamako mai kyau. 

A shekarar da ta gabata fim ɗin Zimbabwe shi ne ya kwashe kyautuka masu tsoka, to a bana mun zuba ido mu ga fim ɗin wacce ƙasa ne zai samu nasara. Muna fatan za mu yi taron lafiya mu tashi lafiya cikin nasara.”

Daraktan Taron KILAF