Daga AISHA ASAS
Yayin da ƙasar Nijeriya ke cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai, al’umma na tofa albarkacin bakinsu kan cigaba, matsaloli da kuma ra’ayoyinsu kan yadda ake tafiyar da mulki a ƙasar nan. Da wannan ne za a iya cewa, kowa na amfani da na sa ra’ayi wurin tofa albarkacin bakinshi, domin wasu kan yi amfani da matsin rayuwa, da yadda talauci ke yi wa al’ummar Nijeriya ɗaurin minti wurin nuna fushi da aibata duk wata gwamnati da suke ƙarƙashin mulkinta.
A wani ɓangare kuwa, wasu kan auna lamarin kan ma’aunin adalci ta yadda za su yabe wasu, su ɓaci wasu, wato ba sa yi masu kuɗin goro.
A wani ɓangare kuma, mutane na murnar zagayowar ranar ‘yancin ƙasarsu ta gado, wasu kuwa suna ganin babu wani abin murna dangane da ranar, sakamakon gani da suke yi ba wata tazara tsakanin mulkin mallaka da aka yi wa ƙasar a baya, da kuma irin mulkin da ake yi a yanzu.
A ɓangaren jarumi a masana’antar Kudu, wato Nollywood nasa ra’ayin ya bambanta da na waɗanda muka ambata, domin shi bai tsaya raba tsakuwa da aya ba, ko yin kuɗin goro a shugabancin ƙasa ba, ya bayyana shi karan kansa shi ne gwamnatin kansa.
A wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumunta, Chidi ya yaba wa ‘yan Nijeriya kan namijin ƙoƙarin da suke yi na samarwa kansu ababen more rayuwa, sakamakon gazawar gwamnati, inda ya ce, “Ku ne gwamnatin kanku.”
“Ina taya kowanne ɗan Nijeriya murna, wanda duk da gazawar gwamnati, sun yi ƙoƙarin samarwa kansu da tsaro a tsakaninsu, ilimi da kuma lafiya, abinci, walwala da kuma wutar lantarki. Don haka koda kuwa 0-1-0 ne, to fa ku ne gwamnatin kanku.”
Jarumin mai shekaru 52, ya kuma yi kakkausar suka ga gwamnatin Tarayya kan rashin iya samar da ababen more rayuwa ga ‘yan ƙasa.
Jarumin wanda ya haska a shirin ‘Shanty Town’, ya bayyana rayuwarsa a matsayin misali, inda ya bayyana gazawar gwamnati da ta tilasta shi samarwa kansa wutar lantarki, ruwa, tsaro, lafiya da kuma ilimi.
“Dangane da wutar lantarki, ni ne da kaina na samar wa kaina taransifoma, da cabe, kuma ni na samar wa kaina mita. Duk da cewa waɗannan ababen da na samar ababe ne da suka rataya wuyan gwamnati, hakan bai hana kuma ni ɗin dai ne zan biya kuɗin kula da su,” ya rubuta a shafinsa na Instagram.
Ya ƙara da cewa, “ har wayau kuma ni ne dole na samarwa kaina janareta, kuma in siye mai a farashi mafi tsada, don kunna janaretana, in samarwa kaina wuta.
A ɓangaren ruwa kuwa, na samar da bohol don amfanin kaina, na samar da famfuna, na samar da tankunan ajiye ruwa, da kuma injimin zuƙo ruwan. Har wayau dai sai na sake siyan mai da tsada don samun damar zuƙo ruwan su iso gare ni.
Domin tsaro kuwa, ni na samarwa kaina get na gidana, da na titi. Ni na samar da get na shigowa gidajenmu, na samar da masu tsaro da za su yi gadin dukka waɗannan ƙofofin, bayaga haka muna komawa ga ubagiji da roƙon kada mu haɗu da harsashen da zai same mu idan muka fita.
Shi ilimi ko? Kayan more rayuwa kuma? Cigaba ko? Gwamnati ta ƙwarai ko? Don haka ko suna so, ko ba sa so, ni ne gwamnatin kaina.”