Daftarin da ya shafi Jihar Xinjiang na da nufin daƙile ci gaban ƙasar Sin

Daga CMG HAUSA

Majalisar kare haƙƙin bil Adama ta MƊD, ta yi watsi da wani daftari da ya shafi jihar Xinjiang, wanda wakilin Sin ya bayyana a matsayin wani yunƙuri na amfani da hukumomin kare haƙƙin ɗan Adam, domin tsoma bakin cikin harkokin cikin gidan Sin, da amfani da batutuwan da suka shafin Xinjiang domin daƙile ci gaban ƙasar.

Chen Xu, shugaban tawagar ƙasar Sin a ofishin MƊD dake Geneva ne ya bayyana haka, inda ya ce Amurka da wasu ƙasashe ne suka shirya tare da gabatar da daftarin, suka kuma miƙa shi a matsayin matsalar dake buƙatar gyara, a yunƙurinsu na gaskata nazarinsu da ya sabawa doka, da sanya batutuwan da suka shafi Xinjiang da babu su a zahiri, a cikin ajandar majalisar.

Ya bayyana gabanin kaɗa ƙuri’a a jiya Alhamis, a zama na 51 na majalisar kare haƙƙin bil Adama cewa, batutuwan da suka shafi Xinjiang, ba su da alaƙa ko kaɗan da na haƙƙoƙin ɗan Adam, yana mai cewa, batutuwa ne da suka shafi yaƙi da ta’addanci da ra’ayi mai tsauri da kuma yaƙi da ‘yan a-ware.

Ya kuma shaida wa majalisar cewa, bisa namijin ƙoƙarin da aka yi, ba a samu ayyukan ta’addanci a Xinjiang ba, cikin shekaru 5 a jere.

Kuma ana ba da cikakkiyar kariya ga haƙƙoƙin dukkan ƙabilun dake jihar.

A cewar Chen Xu, cikin sama da shekaru 60 da suka gabata, yawan al’ummar Uygur na Xinjiang ya ƙaru daga miliyan 2.2, zuwa kusan miliyan 12, kuma matsakaicin shekarunsu na rayuwa ya karu daga 30 zuwa 74.7.

Ya ce ta hanyar yin biris da shaidu da gaskiya, Amurka da sauran wasu ƙasashe sun shirya tare da yada ƙarairayi da jita-jita, a yunƙurinsu na ɓata sunan Sin da kawo cikas ga zaman lafiya a jihar Xinjiang da daƙile ci gaban ƙasar.

Ya ce wannan misali ne na kulli irin na siyasa da take haƙƙin ɗan Adam mai tsanani, na dukkan ƙabilun jihar Xinjiang.

Bugu da ƙari, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin ya bayyana a jiyan cewa, shaidu sun nuna sau da dama cewa, siyasantar da batun haƙƙin ɗan Adam, da nuna fuska biyu, ba za su yi tasiri ba, kuma yunƙurin amfani da batutuwan da suka shafi jihar Xinjiang domin durƙusarwa ko daƙile ƙasar Sin ba zai yi nasara ba.

Mai fassara: Fa’iza Msutapha