Sin ta yi kira da a taimaka wa gwamnatocin ƙasashen Afirka wajen inganta ƙarfinsu na amfani da albarkatun halittu

Daga CMG HAUSA

Mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MƊD Dai Bing ya bayyana cewa, ana samun albarkatun halittu masu yawa a nahiyar Afirka, kuma akwai kyakkyawar makoma a wannan fanni, sai dai ya kamata ƙasa da ƙasa su taimakawa gwamnatocin ƙasashen Afirka, wajen inganta ƙarfinsu na amfani da albarkatun halittu, da kuma sa ƙaimi ga kafa tsarin darajar albarkatun duniya bisa adalci.

Dai Bing ya bayyana hakan ne a jiya, a gun muhawara na kwamitin sulhu na MƊD kan batun yaƙi da ƙungiyoyin ɓata gari da ‘yan ta’adda, waɗanda suke tattara kuɗi ta hanyar fasa ƙaurin albarkatun halittu.

A cewarsa, inganta ƙarfin gwamnati kan aiwatar da harkokinta, zai rage yawan laiffukan fasa ƙauri.

Ya ce ya kamata ƙasa da ƙasa su goyi bayan gwamnatocin ƙasashen Afirka wajen taka muhimmiyar rawa a fannin amfani da albarkatunsu don inganta ƙarfinsu a fannonin tsara shirye-shiryen raya sana’o’i, da sa ido ga hada-hadar kuɗi, da aiwatar da ayyuka bisa doka da sauransu, yana mai cewa ta hakan, za a iya amfani da albarkatu wajen samun ci gaba.

Dai Bing ya ƙara da cewa, samun ci gaba mai ɗorewa ba tare da la’akari da bambance-bambance ba, shi ne tushen samun zaman lafiya da ƙarƙo mai ɗorewa.

Kuma Sin tana fatan ƙasa da ƙasa musamman ƙasashe masu ci gaba za su cika alƙawarin su na ƙara taimakawa ƙasashen Afirka wajen kawar da talauci, da tabbatar da wadatar abinci, da gina ayyukan more rayuwa, da sa ƙaimi ga ba da ilmi da samar da ayyukan yi da sauransu, don ba su gudunmuwa ta haƙiƙa wajen samun ci gaba.

Mai fassara: Zainab