Ƙasar Sin ta miƙa ɗakin adana magunguna na zamani ga Zimbabwe

Daga CMG HAUSA

Ƙasar Sin ta miƙa wani ɗakin adana magunguna na zamani da darajarta ta kai miliyoyin daloli ga gwamnatin ƙasar Zimbabwe, domin bunƙasa ƙarfin ƙasar na adana magunguna da inganta tsarin bayar da kiwon lafiya.

Dakin adana magungunan, wanda ƙasar Sin ta gina tare da samar da kuɗin aikin, ya laƙume dalar Amurka miliyan 22, kuma an yi masa mazauni ne a asibitin Sally Mugabe dake birnin Harare, wanda shi ne asibiti mafi girma na biyu a ƙasar.

Da yake jawabi yayin bikin ƙaddamarwar da mika ɗakin, shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya yabawa ƙasar Sin bisa taimakon da take ba ƙasar a ɓangaren lafiya.

Ya ƙara da cewa, irin wannan goyon baya da tallafi, na nuna karfin alaƙar dake tsakanin ƙasashen biyu, yana mai cewa ƙasarsa na godiya ga Sin, kuma sabon ɗakin adana magunguna ya kai matsayin inganci na ƙasa da ƙasa.

Harabar ɗakin ajiyar wadda ɗaya ne daga cikin mafi girma a kudancin Afrika, ta kai murabba’in mita kimanin 43,000, sannan faɗin ginin ya kai murabba’in mita 13,700. An fasalta shi ta yadda zai iya ɗaukar kantoci 10,000 daga 6,000 da ake da shi yanzu haka.

A cewar shugaba Mnangagwa, karin zai taka muhimmiyar rawa wajen ƙara ingancin samun magunguna a tsarin kiwon lafiya na ƙasar da kuma ƙara inganta ƙoƙarin samar da kiwon lafiya ga kowa.

Mai fassara: Fa’iza Mustapha