Dalilinmu na ƙin tura jirgin yaƙin Tucano Arewa Maso Yamma – Fadar Shugaban Ƙasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Fadar Shugaban Ƙasar Nijeriya ta bayyana cewa, kafin a aike da jiragen saman yaƙi na Tucano da aka sayo daga Amurka a yankin Arewa Maso Yamma, wanda ’yan bindiga suka mamaye, akwai buƙatar a bi ƙa’idojin sayen jiragen, domin kada Nijeriya ta kasance cikin baƙin littafin Ƙasar Amurka.

Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke gabatar da wani shiri a gidan talabijin na Trust.

“Sojojinmu ƙwararren soja ne. Shugaban ƙasa ne ke da alhakin. Idan ya gama yanzu, muna son ya je Kaduna ko Daura ne ya huta, ba ma son ya je kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ba wannan ba ne burinmu. Ya kamata mu bar sojoji su yi amfani da tsarinsu wajen tunkarar waɗannan abubuwa,” inji shi.

Dangane da abin da gwamnati ke yi na ceto fasinjojin jirgin da aka sace daga Abuja zuwa Kaduna, Shehu ya bayyana cewa, sojoji na da ƙarfi sosai a yankin ‘yan ta’addan idan sun ga dama, amma ƙudurin kuɓutar da su a raye yana hana gwamnati shiga cikin lamarin duk wani aikin soja.

Ya ce, gwamnati tana kuma sanya hannun jari sosai kan fasahar jiragen sama, yana mai cewa, “ana samun nasara sosai da jiragen.”

Ya ƙara da cewa, titin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna a shirye ya ke don sake cigaba da aiki bayan harin na baya-bayan nan, “amma tare da kariya daga sama daga rundunar sojojin saman Nijeriya har zuwa lokacin da za a samu fasahar da ta dace da jirgin.

Ya ce, an dakatar da ayyukan jiragen ƙasa ne domin kada a nuna halin ko in kula ga iyalan waɗanda abin ya shafa.

Akan dalilin da ya sa aka shirya ƙidayar al’ummar ƙasar nan a shekarar 2023 duk da ƙalubalen tsaro, ya ce, kamata ya yi a goya wa gwamnati baya kamar yadda ta gudanar da zaɓen Anambara duk da matsalar tsaro a jihar.