’Yan Nijeriya 43,000 ne za su samu damar yin aikin hajjin 2022

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Bayan shekaru biyu da ayyukan sauke farali na aikin Hajji ya ci tura sakamakon hani ga haka da hukumomin Saudi Arabia suka yi domin guje wa yaɗuwar cutar Korona ko ‘COVID-19’ a turance, ‘yan Nijeriya ƙalilan da ba su wuce adadin 43,008 ne kacal aka ba su damar yin ayyukan Hajji na wannan shekara ta 2022.

Kwamishina mai jiɓantar manufa, ma’aikata da lamuran kuɗaɗe (PPMF) na Hukumar Kula da Zirga-zirgar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON), Alhaji Nura Hassan Yakasai shine ya tabbatar da wannan lamari wa manema labarai, yana mai cewar, hukomimin saudiyya sun karɓi kason Nijeriya na maniyyata 43, 008 waɗanda aka amince su yi ayyukan Hajji daga ƙasar nan a wannan shekara da muke ciki.

“Adadin maniyyata 43, 008 daga Nijeriya suna cikin mahajjata miliyan daya da suka haɗa dana wasu ƙasashe, daman a ƙasar ta Saudi Arabia da hukumomin Saudiyya suka amince su gudanar da aiyukan hajji a wannan shekara ta 2022.”

Bayan da ƙasashen duniya har da Nijeriya suka yi rashin zuwa sauke farali a shekarun 2020 da 2021 bisa hani dangane da cutar sarƙewar numfashi ko korona, maniyyata sama da 150, 000 ne da suka haɗa da waɗanda suka yi rajistar zuwa aikin na sherarun 2020 da 2021waɗanda kuma basu samu sukunin zuwa ba, suke sanya ran zuwa sauke farali a wannan shekara ta 2022.

Kason na maniyyata 43,008 babu shakka zai sanya hukumar jigilar alhazai ta ƙasa (NAHCON) da Hukumar kula da lamuran alhazai ta jiha, haɗi da masu safara masu zaman kansu cikin matsanancin yanayi wajen zaɓar adadin maniyya 43, 008 da aka ƙayyade su gudanar da aikin hajji a wannan shekara.

Ƙasar Saudi Arabia dai, idan za a iya tunawa, ta taƙaita maniyyata aikin hajji na shekarun 2020 da 2021ya zuwa ga ‘yan ƙasar ta kadai domin hana yaɗuwar curar Korona.

Sama da alhazai miliyan 2.4 ne da suka haɗa dana jiragen yawo suka gudanar da aikin hajji a shekara ta 2019. Saboda haka, jimlar maniyyata miliyan ɗaya da aka amince su gudanar da ayyukan hajji a wannan shekara ta 2022 suna ƙasa da kashi 50 cikin ɗari na waɗanda suka gudanar da aikin hajji a shekara ta 2019.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *