‘Yan bindiga sun halaka sabon kansila a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wasu mutane akan babura su kimanin 10 da ake kyautata zaton ɓarayin daji ne sun kutsa kai a garin Gozaki dake Ƙaramar Hukumar Ƙafur ta jihar Katsina inda suka afka gidan Alhaji Nasiru Magaji zaɓaɓɓen Kansila a jam’iyyar APC suka kuma hallaka shi tare da yin awon gaba da matansa biyu.

Majiyoyi daga garin na Gozaki sun shaida wa Manhaja cewar lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:30 na daren ranar Laraba lokacin da mutanen garin ke tsaka da barci.

Marigayi Magaji yana ɗaya daga cikin sabbin kansiloli da Gwamna Masari ya rantsar kimanin mako guda da ya wuce bayan da hukumar zaɓen jihar ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe kujerar kansila na mazaɓar Gozaki a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da ya gudana ranar 11 ga watan Afrilu, 2022.

Tun da farko ‘yan bindigar sun yi awon gaba da matan marigayin su 2 zuwa cikin daji kafin daga bisani suka sako su kamar yadda majiyar mu ta shaida.

“Ɓarayin daji sun shigo garin mu da misalin 12:30 na dare suka kuma kashe mana sabon kansilan mu Alhaji Nasiru Magaji wanda ake kira Nasiru B.S,” inji majiyar da muka sakaya sunanta.

An yi ƙoƙarin ceto ran marigayi magaji bayan da aka kai shi babbar asibitin garin Malumfashi, sai dai daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

Kawo yanzu rundunar ‘yan sandan jihar ba ta yi ƙarin haske ba akan harin.

Sai dai mazauna wasu daga cikin ƙananan hukumomi a Jihar Katsina kan bada labarin yadda ‘yan ta’adda ke addabar su, inda suke bayyana cewar kusan kullum ba sa iya runtsawa saboda fargar harin ‘yan bindiga, inda ita kuma gwamnati da jami’an tsaro ke cewa su na bakin ƙoƙarinsu wajen shawo kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *