Gwamnatin Jigawa ta kashe Naira miliyan 22 wajen gina ƙananan gidaje

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Gwamnatin Jihar Jigawa ta kashe Naira miliyan 22 wajen gina gidaje masu sauƙin kuɗi domin amfanin ƙananan ma’aikatan gwamnati. 

Hakan ya biyo bayan karyewar shirin samar da gidaje 40 a kowacce ƙaramar hukuma da gidaje hamsin masu ɗaki biyu wadda Gwamnatin Tarayya ta ɗauki nauyin ginawa tare da haɗin gwiwar bankin Mortgage a Jihar Jigawa farkon zuwan Gwamnatin Badaru shirin ya samh tasgaro.

Yanzu gwamnatin jihar ta ɗauki nauyin shirin samar da gidajen kaitsaye a ɗaukacin ƙananan hukumomin jihar. Saboda haka ne gwamnatin jihar a karon farko ta ware ƙananan hukumomi goma don gina gidajen masu ɗakuna biyu guda huɗu.

Shugaban Hukumar Samar da Gidaje na Jihar Jigawa, Alhaji Mustapha Mohd Umar Ɓaɓura ya ce daga cikin ƙananan hukumomin jihar 27 sun ware goma sun gina gidajen. 

A shiyyar Dutse, Jigawa ta tsakiya, Dutse da Birnin Kudu da Jahun a shiyyar Haɗeja, Jigawa ta Arewa maso Gabas, da Malam Madori da Birniwa.

Sai kuma shiyyar Jigawa ta Yamma maso Arewa, inda ta haɗa da Gumel, Kazaure, Ringim da Ɓaɓura.

Ya ci gabada cewar daga baya an ƙara wasu ƙananan hukumomin guda huɗu da suka haɗa da Ƙaramar Hukumar Maigatari, Sule Tankarkar, Gumel da Kafin Hausa da Auyo.

Amma shekarar data gabata ruwan sama ya yi awon gaba da gidajen Ƙaramar Hukumar Auyo da aka gina.
Su kuma bankin bada rance na Jihar  Jigawa shine ya gina gidajen huɗu da nufin bai wa ƙananan ma’aikata bashin gidajen.

Ya ci gabada cewar yanzu shirye-shiryen ya yi nisa na sake cigaba da gina wasu gidajen a wasu ƙananan hukumomin jihar 16, inda daga cikinsu aka kusa kammala gidaje goma kuma dukkansu masu ɗakuna biyu.