Dandalin shawara: Ina ɗauke da cutar Ƙanjamau da mijina ya mutu ya bar ni da ita, kuma yanzu Ina son aure

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Assalamu alaikum wa rahmatulla. ‘yar’uwa barka da ranar Juma’a mai albarka. Allah Ya raya zuri’a. Ya ayyuka. Dan Allah sirrina zan faɗa ma ki, duk da na san ba ki bayyana suna. Wallahi Ina ɗauke da cutar Sida. Kuma Allah ne sheda ban same ta ta hanyar banza ba.

Mijina a wurin yawace-yawacensa ne ya kwaso ta, ya zo ya sa mun. ban san Ina da ita ba, sai ranar da ya sanar da ni yana tare da cutar, kuma ya shekara biyu da ita. to bayyan na tabbatar ni ma na samu, muka shiga shan magani asiri rufe. Sai dai a shekarar baya ne ya zo ya rasu, na yi fargaba da sauran su yanzu kuma na kwaɗaita da son aure, don Ina da sauran ƙurciyata.

Duk yadda zan cire abin na yi, amma kin san sha’ani na sha’awa, ya bar mun dukiya ni da ‘ya’yana wanda ya sa manema ke ta zuwa, sai dai Ina tsoron sanar da su kan matsalata don gudun su qi amincewa kuma su je su fallasa. Ki taimaka mun da shawara yadda zan samu biyyan buƙata ta ba tare da asirina ya tonu ba, kin dai san yadda ake ƙyamar masu ciwon. Na gode, Allah Shi yi albarka.

AMSA:

Wa’alaikumus salam warahmatulla wa barakatuhu. Kafin komai zan so in yi amfani da wannan dama in jawo hankalin mutane ko in ce masu nuna ƙyama marar iyaka ga masu ɗauke da lalurar cutar Ƙanjamau. Da farko dai da yawa cikin mutanenmu musamman a Arewacin Nijeriya sun mayar da wannan cutar ta ‘yan iska, karuwai da mabiɗa mata, don haka da zaran an ce wance ko wane na ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki, to fa daga ranar kallon da ake yi masa ya canza, daga mutumin kirki ko matsakaici zuwa ɗan iska ko ‘yar iska. Saboda sa wa zuciyarsu da suka yi ba wanda yake iya kamuwa da wannan cuta sai masu neman mata ko mace mai bin maza.

Likitoci da malamai da dama sun sha shelanta hanyoyin kamuwa da wannan cuta wadda ba dole sai ta saduwa ba, kuma sun sha faɗakarwa kan hulɗa da masu cutar, don haka na san da yawa sun sani, suna dai kunnen uwar shegu ne da abinda suka sani, zuwa abinda suke son ya zama. Wannan zai sa rubutuna ba zai zama baƙo ga wasu mutane ba, duk da hakan zan yi ko a yi nasara kan wasu.

Cutar Ƙanjamau ba cuta ce da za ka iya kamuwa da ita ta mu’amala ta yau da kullum ba, kamar haɗa hannu ko cin abinci, kwanciya a wuri ɗaya, sanya kaya ɗaya da makamantan su. Duk waɗannan ba su sa mai cutar ya sa ma ka. Kenan babu wani dalili da zai sa ka ƙyamace mu’amala da shi.

Za ka iya ɗaukar wannan citar ne ta hanyar jini, ma’ana a lokacin da jininka ya haɗu da na mai cutar, kamar amfani da allurar da mai cutar ya yi amfani da ita, ko reza idan ya yanke kanshi da ita, kai ma ka yanke, ko idan kana da wani ciwo da ya kwaye fatar jikinka sai shi kuma ya ji ciwo, jikin nasa ya taɓa inda ciwon naka yake.

Duk wata hanya dai da zata sa jikinsa ya haɗu da na ka, domin ita HIV wato Human Immunodeficiency Virus a turance ƙwayar cuta ce da ke faɗa da ƙwayoyin halitta na jikin ɗan Adam da ke yaqin kare jiki daga cututtuka, wanda idan sun yi nasara za su bar jiki tsirara, wato ba wata kariya ko wani hijabi tsakaninsa da ƙwayoyin cuta. Ita wannan ƙwayar cutar an fi ɗaukarta ta hanyar saduwa marar kariya, sai dai cigaba ya zo da za a iya mu’amala da mai wannan cutar ta hanyar saduwa ba tare da an ɗauke ta ba, ta hanyar magani.

Ita wannan ƙwayar cuta idan aka ƙyale ta ba tare da maganin kula da yawaitarta ba ne ta ke zama AIDS wato Acquired Immunodeficiency Syndrome kuma shi ne mataki na ƙarshe a wannan cutar, ma’ana dai ta kai matakin nasara, ma’ana ta karya garkuwar jiki iyakar karyawa.

Ita wannan ƙwayar cuta ta HIV garkuwar jiki bata iya kawar da ita, kuma har zuwa yanzu babu takamaiman magani da aka ce ga shi na magance ƙwayar cutar, duk da haka akwai magunguna da suke hana ta rawar gaban hatsi a jikin ɗan Adam, su hanata yaɗuwa da ke kai ga zama AIDS.

Kuma amfani da magungunan na sa mai ƙwayar cutar ya yi rayuwa tamkar babu abinda ke damunsa, asalima idan ba shi ya faɗa ba ba za ka ga alamun ta a tare da shi ba.

Kuma yana daga cikin cigaban da aka samu, iya kusantar mai cutar ta ɓangaren saduwa ba tare da ya ɗauki cutar ba, shima ta hanyar magani, ko kuma waɗanda ke kula da kansu sosai har suka kai matakin da ita wannan ƙwayar cutar ta yi ƙasa sosai, abin da masana ke amfani da kalmar viral load, matsayi ne da yake ma’auni ga yawa ko ƙarancin ƙwayar cutar, idan viral load ɗin ya yi sama ne ake kai ga matakin AIDS, idan ya yi ƙasa sosai ne za a iya kai matakin da ƙwayar cutar take takura ƙwayar cutar har ya mayar da ita ‘yar ƙarama da wasu lokutan ba a cika iya ganinta yayin da aka yi awo, to wannan bata cika zama matsala ko mai yaɗuwa ba, saboda ƙarancinta, sai dai kuwa idan ta samu damar ƙaruwa.

Daga cikin abinda ke taimaka wa wannan ƙwayar cuta wurin mamayar gangar jiki akwai rashin cin abinci mai gina jiki da zai ba wa gangar jiki makaman da ta ke buƙata na yin yaƙin, akwai rashin amincewa da fara shan maganin wannan cuta da wuri, abu na uku kuwa akwai damuwa, wanda akan ta nake so in ɗan maida hankali.

Za mu ci gaba a mako mai zuwa