An cafke makaho ɗan Nijar da safarar miyagun ƙwayoyi

Jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi a Nijeriya (NDLEA) ta sanar da kama wani mutum makaho da ɗansa yayin da suke ƙoƙarin safarar tabar wiwi da miyagun ƙwayoyi.

Cikin wani saƙo da NDLEA ta wallafa a shafinta na Facebook ɗauke da sa hannun Darektan yaɗa labaranta, Femi Babafemi ta ce, an kama mutanen biyu ne a hanyar Malumfashi-Zaria a Jihar Katsina.

NDLEA ta ce, an mahaifin wanda shi ne makahon mai shekaru 52 da ɗansa mai shekaru 30, ɗauke da kilo 20.5 na tabar wiwi da kuma gram 10 na exol-5.

NDLEA ta bayyana cewa asalin mutanen sun fito ne daga Jihar Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar.

Kazalika, NDLEA ta ce jami’anta na sintiri ne suka cafke mutanen a hanyarsu ta komawa Nijar.