Dangane da janye dokar hana amfani da tsofaffin kuɗi

Daga HAFIZ KOZA ADAMU

  1. Na fahimci yanzu sababbin takardun kuɗi suna ƙaranci saboda yawaitar tsofaffin takardun kuɗin. A nan sai tunanina ya ba ni to ko masu tsofaffin ne ke fito da ajiyayyun kuɗaɗensu, suna amsar sababbin suna sauyawa, sai kuma sababbin suna sake mai da su ma’ajiya tun da har yanzu ana kan dokar cewa, zuwa Disambar bana za a daina hada-hada da tsofaffin? Idan kuwa haka ne, rufa ta yi, ba ta mutu ba!
  2. Na fahimci bankuna ba su cika samun masu shigar da kuɗaɗe ba, mafi akasarin masu zuwa banki ko dai wata matsala ce ta kai su, ko kuma sun je cire kuɗi (withdrawal) amma ba ajiye kuɗin (depositing) ba. Idan kuwa haka ne, da an ƙwalƙwale kuɗaɗen da ke a bankuna (Ciki har da CBN da ke bai wa bankunan kuɗi), duk za su zama fanko; su kasance wuraren amsar ƙorafi amma ba na hada-hadar kuɗi a kuɗance ba.
  3. Na fahimci mutane za su koma yin ajiyar garin kuɗaɗensu a gida ko wata ma’ajiya maras tabbas, domin suna tsoron kai kuxin banki idan sun je nema su sha wahala. Hakan na iya dawo da ayyukan fashi da makami a gidajen masu akwai.
  4. Na fahimci fatake waɗanda a baya suka rungumi hanyar sanya kuɗaɗensu a asusun banki, su kamo hanyar kasuwa ba tare da kuɗi ba, saboda gudun ‘yan-kwanta-kwanta da ke zambatarsu a kan titin, yanzu suna tarar aradun jimƙo kuɗaɗensu ne su kamo hanya da su, domin rashin kuɗin a hannu yana ta’azzara tsadar kayan da suke saye a kasuwanni. Wannan kasadar ma za ta iya dawo da ayyukan miyagu da ke kwanta-kwanta.

Bayan tawa nau’in fahimtar wacce kuke hangowa, ko kuma shin tawa fahimtar tana daidai ne ko akasin haka?

Hafiz Koza Adamu, ɗan ƙasa ne mai bayyana ra’ayi. Ya rubuto daga Katsina.