Dangote zai gina tashar jiragen ruwa mafi girma a Najeriya a jihar Ogun

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko ɗangote, ya mika takardun neman izinin gina tashar jiragen ruwa mafi girma da zurfi a faɗin Nijeriya a jihar Ogun.

Da yake tattaunawa da jaridar Bloomberg ta Birtaniya, attajirin na Afrika ya ce tuni ya aike da buƙatar tasa domin fara aiki a ga ar ruwa ta Olokola da ke jihar ta Ogun.

Ya ce gina tashar zai taimaka wajen sauƙaƙa fitar da kayayyaki waje daga Nijeriya, ciki har da makamashin gas da kuma bunƙasa rukunin masana’antunsa.

Ya ce tuni yunƙurin nasa ya yi nisa inda tun a watan da ya wuce ya mika takardun neman amincewa da buƙatar tasa.

“Ba wai so muke a ce mun mamaye komai ba, amma ina kyautata zaton yin hakan zai karfafa gwiwar sauran masu zuba jari su ma su zo su yi hakan,” inji shi.

Gina sabuwar tashar dai nan una dawowar Dangote filin da a baya ya yi watsi da shi, bayan tun da farko a can ne ya ƙuduri aniyar gina matatar man shi da kamfanin sarrafa takin zamani, kafin saɓanin da ya samu da mahukuntan jihar ya say a dakatar da shirin.

A ƙarshen watan Mayun da ya gabata kamfanin na ɗangote ya sanar da cewa yana hanƙoron samun Dalar Amurka miliyan bakwai a kullum daga sayar da takin zamani a nan da shekaru biyu masu zuwa.

Wata ɗaya bayan haka kuma, ya sanar da far araba man dizal da na fetur a ranar 15 ga watan Agusta mai zuwa, inda tuni har ya kawo motoci masu amfani da gas guda 4,000 domin aikin rarraba man a faɗin Nijeriya.

By ukarofi