Gyaran matatun man Nijeriya kamar sabunta tsohuwar mota ne – Dangote

Spread the love

Daga MAHDI MUSA NUHAMMAD

Hamshaƙin attajirin ɗan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote ya koka game da makomar matatun gwamnatin Nijeriya, inda ya ce duk da Dala biliyan 18 da aka kashe wajen gyara su, ba lallai su koma aiki kamar yadda su ke a baya ba.

Dangote a yayin ganawa da wata tawaga daga shirin ‘Global CEO Africa Programme’ na
Makarantar Kasuwanci dake Legas, ya ce zai yi wahala matatun Fatakwal, Warri da Kaduna da ke ƙarƙashin kamfanin NNPCL su sake koma wa aiki yadda dace.

Ya ce, an ɗauki shekaru ana ɓarnatar da kuɗaɗe domin dawo da martabarsu duk cewa gwamnatoci da dama sun ta yin alƙawarin gyara su.

A yayin zagaye matatarsa mai fitar da ganga 650,000 a kullum dake Lekki, wanda ake ganin mafita fame da matsalolin shigo da fetur daga waje, Dangote ya bayyana bambanci aiki da ke tsakanin tasa da na gwamnati.

Ya kuma hakaito yadda kamfaninsa ya saye matatun a shekarar 2007 lokacin da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ke shirin barin mulki.

Watanni kaɗan bayan haka ne a lokacin marigayi tsohon shugaban ƙasa Umar Musa Yar’Adua aka rushe cikin, bayan wasu jami’an NNPC sun faɗa wa Yar’Adua cewa an sayer da su ne a farashi mai rahusa.

“Ko da kun maye gurbin injin ɗin, jiki ba zai iya ɗaukar girgiza wannan sabuwar fasahar ba,” inji shi, yana mai jaddada tsufa na kayan aiki.

Wannan ra’ayi ya yi daidai da ra’ayoyin da tsohon shugaban ƙasa Obasanjo ya yi a baya, wanda a cikin jawabai da dama a bainar jama’a a cikin shekaru biyu da suka gabata ya nuna matuƙar bacin ransa kan halin da matatun man ke ciki.

A baya Obasanjo ya bayyana cewa ya shawarci magajinsa da kada ya soke sayar da matatun, inda ya yi gargadin cewa NNPC ba ta da ƙarfin tafiyar da su.

“NNPC sun san ba za su iya ba, amma sun so su ci gaba da cin hanci da rashawa da rashin aiki,” inji Obasanjo yayin wata hira da 2023.

“Shell ya ƙi gudanar da ayyukan matatun man, sun ce min ba za a yi ciniki da shi ba, amma mutane a NNPC sun ce ba haka ba.”

Ya ƙara da cewa, dala miliyan 750 da Dangote da haɗin gwiwarsa suka biya domin sayen matatun, kimantawa ce ta hakika, ba “kyauta” ba, kuma yunƙurin sayar da su nan gaba na iya samun wani kaso na wannan farashin a matsayin guntun kuɗi.

“Lokacin da kuke son sake sayar da su, ba za ku sami ko dala miliyan 200 ba,” Obasanjo ya yi gargaɗin.

Hankalin jama’a game da matatun ya kai wani sabon matsayi bayan da matatar mai ta Fatakwal, wacce hukumar NNPCPL ta ayyana “aiki a wani ɓangare” a ƙarshen 2024, an sake rufe ta cikin nutsuwa bayan watanni shida kacal. Matatar mai ta Warri, wacce aka sake buɗewa a watan Disamba 2024, ita ma ta daina aiki cikin wata guda.

By ukarofi