Darajar masana’antar intanet ta ƙasar Sin zai kai Yuan tiriliyan 4.45 a 2022

Daga CMG HAUSA

Cibiyar nazarin masana’antar intanet ta ƙasar Sin, ta fitar da takardar bayani game da ci gaban tattalin arzikin masana’antar intanet ta ƙasar, inda ta yi hasashen cewa, darajar masana’antar za ta kai yuan triliyan 4.45 a bana, wanda zai kai kaso 3.64 na alƙaluman tattalin arziki na GDP na kasar.

A yanzu, masana’antar ta shiga cikin harkokin tattalin arziki da suka shafi hada-hadar kuɗaɗe kai tsaye, wanda ya shafi rukunoni 45 na tattalin arzikin ƙasar.

A shekarar 2021, darajar masana’antar a wannan fanni, ta kai yuan triliyan 2.93, inda aka yi hasashen darajarta a bana za ta kai yuan triliyan 3.16.

Baya ga haka, masana’antar na daukaka tsarin samar da ayyukan yi a ƙasar tare da daidaita ci gaban ɓangaren.

An yi kiyasin za ta samar da sabbin guraben ayyukan yi fiye da miliyan 1 da dubu 50 a bana.

Gu Weixi, mataimakin daraktan cibiyar nazarin masana’antar intanet ta ƙasar Sin, ya ce masana’antar ta taka muhimmiyar rawa wajen daidaita tsarin samar da kayayyaki, kuma tana bayar da gagarumin taimako ga ɓangaren tattalin arziki na zamani.

Mai fassara: Fa’iza Mustapha