Daga CMG HAUSA
Kwanan nan ne ministocin harkokin wajen ƙasashe mambobin ƙungiyar G7, suka fitar da wata sanarwar haɗin-gwiwa a birnin Münster na ƙasar Jamus, sanarwar da ta jibanci harkokin cikin gidan ƙasar Sin, ciki har da batutuwan da suka shafi Taiwan, da Hong Kong, da Xinjiang da kuma Tibet.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin, Zhao Lijian, ya bayyana a yau Litinin 7 ga wata cewa, sanarwar ta yi biris da babban matsayin ƙasar Sin, gami da hakikanin abubuwan dake faruwa, inda ta yi katsalandan cikin harkokin gidan ƙasar, da shafawa kasar bakin fenti, al’amarin da ya janyo matuƙar rashin jin dadi da adawa daga ƙasar Sin.
Zhao ya ce, ƙasarsa ta buƙaci ƙungiyar ƙasashen G7, da ta yi fatali da ra’ayin cacar baki, da bambancin ra’ayin da take nunawa har kullum, da datakar da tsoma baki cikin harkokin gidan sauran ƙasashe, ko kuma maimaita ƙarairayi, da daina rura wutar rikici tsakanin ɓangarori daban-daban, a wani ƙoƙari na ƙirƙiro kyakkyawan sharadi ga hadin-gwiwar ƙasa da ƙasa.
Mai Fassara: Murtala Zhang
