Sojoji sun kashe shugabannin ’yan ISWAP a tafkin Chadi

Sojojin Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar Sojojin Nijeriya sun samu nasarar halaka wasu manyan shugabannin ƙungiyar ta’addancin ISWAP, Ali Kwaya da Bukar Mainoka a Tafkin Chadi.

An kashe su ne a wani samame da jiragen yaƙin sojin Nojeriya suka kai a tafkin Chadi a ranar Asabar.

Kwaya da Mainoka, waɗanda kuma su ne jagororin ’yan ƙungiyar ISWAP Shura (Consultation) Council sun baƙonci lahira a lokacin da Rundunar Sojan Sama na ‘Operation Hadin Kai’ ta gudanar da aikin ceto a Belowa, ɗaya daga cikin ’yan tsirarun da suka rage na ISWAP/Boko Haram a Tumbuns. Yankin tafkin Chadi a ƙaramar hukumar Abadam.

An ruwaito wani jami’in leƙen asiri na soji yana cewa, harin da suka kai ta sama a Belowa ya zama dole bayan bayanan sirri sun nuna haɗuwar wasu shugabannin ISWAP da mayaƙansu a kewaye da wurin su na ganawa da manufar shirya kai hare-hare.

A cewar jami’in wanda ya nemi a sakaya sunansa, jirgin yaƙinsu na rundunar sojojin saman Nijeriya (NAF) ya afka wurin taron ’yan ta’addan a Belowa, inda ya yi artabu da ’yan ƙungiyar ta ISWAP da rokoki da bama-bamai.