Barazanar hari: ‘Yan Birtaniya na iya ziyartar Abuja – Ofishin Jakadanci

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Birtaniya ta ce yanzu ‘yan ƙasar za su iya ziyartar babban birnin Nijeriya, Abuja, ba tare da wani tsoro ba.

A ranar 23 ga Oktoba ƙasar ta yi gargaɗin ‘ya’yanta su ƙaurace wa Abuja saboda barazanar harin ta’addanci.

Ofishin Jakadancin Birtaniya da ke Abuja, ya gargaɗi ‘yan ƙasar da su yi taka-tsan-tsan da zamansu a birnin na Abuja.

Sai dai kuma, cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na intanet a ranar Litinin da ta gabata, ofishin Jakadancin ya ce ‘yan ƙasar na iya ziyartar Abuja duk da dai hadarin barazanar bai gushe ba.

Amma ya ƙarfafa kan ‘yan ƙasar su guji zuwa jihohi da suka haɗa da; Borno, Yobe, Adamawa, Gombe, Kaduna, Katsina, Zamfara da kuma jihohin da ke bakin ruwa irin su Delta, Bayelsa, Ribad, Akwa Ibom da kuma Kuros Riba.