Zaɓen 2023: Arewa ina aka dosa?

Spread the love

Ban san gaibu ba, amma ga dukkan alamu yankin Arewa na da jan-aiki gabanin zaɓe mai zuwa.

Tun da farko qungiyoyi na arewa a bisa jagoramcin Sakataren ta Mal Murtala Aliyu. Sun tsara tare da aiwatar da zama da ’yan takara da a ke kallon su ne a sahun gaba domin miƙa ma su muradu da sharuɗɗan yankin Arewa. An aiwatar da wancen zama a Arewa House na Jihar Kaduna.

Ana nan sai mu ka ji wani jigo a wasu gamayyar ƙungiyoyin na arewa mai suna Dr Auwal Abdullahi Aliyu ya fito a wata tattaunawa da wakilin BBC Hausa, Abdussalamu Ibrahim Ahmed inda wance jagora yai ƙorafi na cewa zaman farko da su ACF su kai tamkar bai da wani tasiri wai ba a gayyato su a zaman ba.

Hakan ne ƙara nakasa kimar Arewa middin ba mu sasanta kanunmu a gida. Haka na a dai BBC Hausa a ranar assabar kwana

guda bayan ɗan takara na APC Tinubu ya ayyana fara yaƙin neman zaɓe. Mun ji wani jigo a ƙungiyar CAN daga Adamawa ya soki tsarin na Musulmi da Musulmi.

Daga MUKHTAR IBRAHIM SAULAWA. 07066434519.

By Editor