Sojojin ruwa sun fara aikin hizba a Fatakwal, sun afka wa gidan karuwai, sun tserar da ‘yan mata 50

Daga WAKILINMU

Kimanin ’yan mata sama da hamsin ne aka kuɓutar a gidan karuwai tare da kama wasu mutane uku da ake zargin masu safarar mutane don jima’i ne a wani samame da jami’an sojin ruwan Nijeriya suka kai a wasu gidajen karuwai biyu a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.

Babban Kwamanda Richard Iginla, Jami’in yaɗa labarai na sansanin sojin ruwa na NNS Pathfinder, ya bayyana hakan a ranar Lahadi ga manema labarai yayin da ya ke gabatar da waɗanda ake zargin a Fatakwal.

Iginla ya ce, an gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar hukumar hana fataucin mutane ta Nijeriya (NAPTIP) da kuma jami’an NSCDC.

A cewarsa, karuwai 50, galibi ’yan mata matasa ne aka ceto da sanyin safiyar Asabar bayan da hukumar NAPTIP ta samu labarin.

“Mun samu bayanan sirri ne daga hukumar ta NAPTIP, wacce ta riƙa bin gidajen karuwai da suka yi garkuwa da yara waɗanda galibinsu ’yan ƙasa da shekara 14 ne.

“Don haka, bayan da hukumar NAPTIP ta raba mana bayanan sirri, an kafa wata tawaga ta haɗin gwiwa, nan ta ke muka shiga aikin ceto waɗanda lamarin ya shafa.

“An ceto ‘yan mata sama da 50 da aka tilastawa yin karuwanci yayin da aka kama masu ɗaukar ma’aikata uku da masu gudanar da ayyukan karuwanci,” inji shi.

Iginla ya ƙara da cewa, an rufe gidajen karuwai na; Royal Brothel da Cool Breeze Brothel da ke kan titin Azikiwe a unguwar Diobu a Fatakwal.

Ya ce, kuma ana cigaba da ƙoƙarin zaƙulo shugabannin ƙungiyar masu safarar mutane domin jima’i tare da kame ƙananan yara daga ƙauyuka suna tilasta su yin karuwanci.

“Yara kyau ne daga Allah, kuma dole ne mu yi duk abin da zai yiwu don kare su daga kowane irin cin zarafi.

“Rundunar sojin ruwan Nijeriya za ta cigaba da haɗa kai da hukumomin da abin ya shafa domin gurfanar da masu aikata laifukan da ke safarar mutane a ƙasa ko ta hanyar ruwa.

“A ƙarshen bincikenmu, za a miƙa waɗanda ake zargi da waɗanda abin ya shafa ga hukumar NAPTIP domin cigaba da bincike da kuma gurfanar da su a gaban kotu,” inji shi.