Da Ɗumi-ɗumi: ‘2023: PDP ba ta da ɗan takara a Zamfara’

Daga SANUSI MUHAMMAD, Gusau

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Gusau a ranar Talata ta soke ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023 da ke tafe a jihar.

Kotun ta bayyana cewa, PDP ba ta ɗan takarar gwamnan a jihar ta Zamfara.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Aminu Baffa ya yanke hukuncin ne yayin zaman kotun kan ƙarar a ranar Talata.

An shigar da ƙarar a gaban kotu wanda Injiniya Ibrahim Shehu Gusau ya yi yana mai ƙalubalantar Jamiyyar PDP, Adamu Maina Waziri, Kanal Bala Mande, Dauda Lawal Dare da kuma hukumar INEC kan wasu kura-kurai da aka tafka a zaɓen fidda gwanin ɗan takarar gwamnan PDP da aka yi a jihar.

Cikakken bayani na nan tafe…