Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Amurka ta shuka zamba shi za ta girba

Daga CMG HAUSA

Rahotanni sun ce, shugaban Amurka, Joe Biden, ya ce zai matsawa ƙasashen Japan da Holland lamba, don buƙatar su hana fasahohin zamani na ƙera ɓangarorin hada na’urorin laturoni su shiga ƙasar Sin.

Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yau Litinin 7 ga wata cewa, abun da Amurka ta yi, ba abu ne da ya kamata wata babbar ƙasa ta yi ba.

Kowa ya shuka zamba, shi zai girba, a cewar malam bahaushe.

Mai fassara: Murtala Zhang