Dandalin shawara: mijina ba ya son yin wanka

ci gaba daga makon jiya

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Aisha an yini lahiya. Allah Shi taimaka, Ya yi ma ki jagora. To ni ma dai da ‘yar neman shawara na taho kamar yadda aka saba yi. Wallahi miji a gare ni da yake warin jiki, babu ma kamar baki nai. Bai son yin wanka. In ya matso ni kamar in yi amai. Shi ya sa duk da Ina son auratayya wallahi har ban sha’awarta, don da ya matso sai warin ya sa abin ya fita daga raina. Kuma matsalar mijin nau na cikin irin hitinanun mazan nan ne da ba su amsar laihi idan an ce sun yi. Ko kan gaskiya kike sai sun maido mi ki laihi. Ga jinini da yawan mita. Don Allah ya kike ganin za a yi kan wagga matsala, don ta isheni. Na gode. ‘yar’uwarki…………….

AMSA:

Yana da matuƙar muhimmanci miji ya kula da yi wa matarsa kwalliya, ba wai dole sai a lokacin barci ba, idan kana gida ka yi kwalliya tamkar za ka wani taro, daidai da yadda ka fahimci matarka na so, wannan ba daudanci ne ko zama mijin hajiya ba kamar yadda kuka ɗauke shi.

Wannan kawai zai ƙara ma ƙima a idon matarka, kuma za ka samu tarairiyya da ƙarin soyayya daga gare ta. Kuma hakan zai sa a kullum tana marmarinka, wanda hakan na nufin ba sai ka dinga ƙaramar murya kamar ta sabon kwarto ba.

Idan kuwa an zo kwanciya, ka tabbatar ka daure ka yi wanka, ko ba halin siyan turaruka masu ƙamshi da ke kwantar da hankalin abokiyar mu’amala, a tabbatar ba wari.

Ka wanke baki da man baki, ta yadda za a kawar da duk wata hanya da wari zai samu wurinm zai yi kutse. Kuma turare komai zamansa mai arha zai taimaka matuƙa wurin samun natsuwa.

Idan mun koma ɓangaren dalilin wannan dogon bayani, wato shawara gare ki mai tambaya, zan iya cewa, hanya ce da sai kin jure, sai dai mai sauƙin samun mafita albarkacin kasancewarki mace, domin baiwa ta ‘yan dabarun tursasa miji yin abin da muke so ko ba ya so.

Wahalar wannan shi ne, ke ce a ƙasa, shi ke da iko da ke, don haka ba zance ne na bada umurni ko faɗa ba. Ga kuma zaman mijin na ki bahago sai da lallami.

A nan zan ce idan kina da sana’a wannan na ɗaya daga cikin amfaninta, domin za ki iya amfani da ‘yan kwabbanki don fara koya wa mijinki tsafta, ta hanyar siya ma shi ‘yan kayan amfani kamar sabulun da ya fi wanda yake kawo wa ƙamshi ko kyau, ɗan turare daidai ƙarfi da kuma abin kawar da warin baki.

Za ki siyo ne a matsayin kyautar masoyiya zuwa ga masoyinta, hakan za ki nuna a bayar da kyautar, in da hali a haɗa da ‘yan kalamai masu tava zuciya.

To da waɗannan za ki yi amfani zuwa mataki na gaba, wato a duk lokcin da ya dawo ki cire ƙyuya ki yi hanzarin kai masa ruwan wanka, ki sanya masa man wanke baki a buroshi ko idan na ruwa ne ki riƙa masa, ki sanar da shi.

Na san a nan ba lallai ku kwashe lafiya ba, tunda ba abin da yake so ba ne, zai yi turjiya, don haka ki kwantar da kai tare da amfani da ‘yar dabar mata. Idan kin lura yana sha’awar ku yi wanka tare za ki iya amfani da wannan damar wurin janyo ra’ayinsa, ta hanyar taya shi wankan duk dare.

Kuma za ki iya ƙoƙarin bambance masa ranar da ya yi wanka da ranar da bai yi ba a kwanciyar auren. Ki tabbatar kin dinga yin wasu ababe da za su zama abin so gare shi, waɗanda a ranar da bai yi wanka ba za ki yi ba.

Ki tabbatar da masu girma ne da za a iya gane rashin su, wanda hakan kawai zai iya janyo hankalinsa ga gane romon tsaftar. Idan ya fito, ya tarar da kayan da ya kamata ya sa wanda kika ɗauki nauyin wanke wa ko bayarwa a wanke, domin wani lokacin ƙazantar maza har da ƙyuya. Saboda haka kayan barcin ya zama kawai nasa sawa da cirewa.

Sannan akwai ‘yan dabaru da mata ke amfani da su wurin aika saƙo ga mazajensu ba tare da sun yi amfani da baki ba, idan kin fahimce ni za a iya samun canji ko ta wannan ɓangare.

Sai dai kamar yadda na faɗa a baya, ba aiki ne na ɗai rana ko lokaci kaɗan ba, dole sai kin sanya haƙuri, domin zai iya ɗaukar lokaci fiye da kike tsamani, kuma idan aka sa addu’a Allah zai iya kawo abin cikin sauƙi ba tare da rayuka sun ta ɓaci ba, kuma cikin ɗan lokaci kaɗan.