Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna zai soma aiki kwanan nan -Minista

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Nijeriya ta ba da sanarwar ranar da jirgin ƙasar Abuja zuwa Kaduna zai dawo bayan da ya shafe watanni bakwai ba ya aiki sakamon harin ‘yan ta’adda.

Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo ya ba da sanarwar hakan inda ya ce jirgin zai koma bakin aiki kwanan nan.

Ya bayyana hakan ne sa’ilin da yake bayanin ayyukan da ma’aikatarsa ta aiwatar ranar Litinin a Abuja.

Ya ce, cikin wannan wata na 11 jirgin zai ci gaba da aiki, tare da cewa an samar da ingantaccen tsaro don kare rayukan fasinjoji.

Idan dai za a iya tunawa, Hukumar Sufurin Jirgin Ƙasa (NRC) ta dakatar da zirga-zirgar jirgin Abuja zuwa Kaduna ne saboda ƙalubalen tsaro.

A ranar 28 ga Maris da ya gabata mayaƙan Boko Haram suka kai wa jirgin farmaki inda suka yi awon gaba da fasinjoji da dama wanda daga bisani aka kuɓutar da su.