FIRS ta fara amsar haraji kai-tsaye daga masu manhajojin wasanni na yanar gizo

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar tattara haraji ta birnin Tarayyar (FIRS) ta fara cirar haraji daga manhajojin wasannin na yanar gizo ta hanyar zarar harajin a duk yayin da suka yi hada-hadar kuɗi.

A wata sanarwar da shugaban zartarwar hukumar, Mista Muhammad Nami ya sanya wa hannu, an bayyana cewa, wannan hukunci na fara zarar harajinta ya samu goyon bayan dukkan mamallakan manhajojin wasannin na yanar gizo.

Shi dai wannan tsari na cire harajin nan take wani tsarin cire haraji nan take ne a duk lokacin da manhajojin wasannin suka yi hada-hadar kuɗin ta banki. Sannan kuma a take a nan harajin zai wuce i zuwa lalitar gwamnatin tarayya.

A halin yanzu dai hukumar ta ba da umarni ga dukkan masu gudanar da gema-geman yanar gizo da su yi rajista da bin tsarinta na harajin nan take (Sentinal National Payment Gateway).