DSS ta cafke ‘Yan Boko Haram a Osun

Jami’an hukumar tsaro ta DSS sun kama mutane 10 da ake zargin mambobin Boko Haram ne a garin Ilesa, Jihar Osun.

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanata Ademola Adeleke, Mallam Olawale Rasheed, ya tabbatar da cewa waɗanda aka kama suna da alaka da Boko Haram da kuma ƙungiyar ISWAP. Ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da haɗin gwiwa da hukumomin tsaro tare da tallafa musu don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Osun.

“Wannan wani gagarumin ci gaba ne kuma babban sauƙi, ba kawai a gare mu a matsayin gwamnati ba, har ma ga mutanen jihar da Najeriya baki ɗaya. Ina yabawa jami’an tsaro bisa ƙoƙarinsu da dabarunsu na bincike. Muna da cikakken tabbaci kan ƙoƙarin hukumomin tsaro wajen kare mu.”