Manyan fitattun jaruman Kannywood na 2024

DAGA MUKHTAR YAKUBU

Shekarar ta 2024 ta zo ƙarshe kuma a yanzu an shiga sabuwar shekara ta 2025 ga mai yawan rai.

Abubuwan da dama sun faru na ci gaba a cikin masana’antar finafinai ta Kannywood tun daga farkon ta zuwa ƙarshen ta waɗanda idan aka ce za a yi bayanin su ɗaya bayan ɗaya za a ɗauki tsawon lokacin ana bayani a kansu.

Amma da yake an ce abin da yawa, wai mutuwa ta je kasuwa, bari mu ɗauki wani ɓangare mafi muhimmanci a cikin harkar fim musamman ga masu kallo. Wannan ɓangaren kuwa shi ne na jaruman da suke fitowa a cikin fim waɗanda su ke a kullum masu kallo suke gani, kuma su ne ma masu kallon suke gani a matsayin harkar fim ɗin bakiɗaya. Don haka muka yi duba da kuma bincike domin fito da jarumai guda 20 da suka yi fice a cikin wannan shekarar ta 2024 da ta ƙare a makon baya.

1. Yakubu Muhammad:

Jarumi Yakubu Muhammad ya daɗe a cikin masana’antar finafinai ta Kannywood a matsayin mawaki, furodusa kuma darakta.

A ‘yan shekarun baya ya rikiɗe ya koma matsayin jarumi, kuma harkar ta karɓe shi, inda ya taka rawa a finafinai da dama har ma da finafinan Turanci.

A wannan shekarar ta 2024 ya kasance jarumin da yake da tasiri a finafinan Kannywood, musamman idan aka duba rawar da ya taka a finafinan ‘Labarina’, ‘Garwashi’, ‘Allura Cikin Ruwa’ da ‘Gidan Sarauta’.

2. Fatima Hussaini:

Tana ɗaya daga cikin jaruman da ta ɗauki hankalin masu kallo a cikin wannan shekarar ta 2024. Domin kuwa rol ɗin da ta taka a cikin shirin ‘Labarina’, ya jawo mata ɗaukaka ya jawo mata tsana daga masu kallo. Domin an sha ƙorafi a kanta da cewar ta fiye iya yi, abu kadan sai ta jefo Turanci, wannan ya zamar da ita fitacciyar jaruma a shekarar 2024.

3. Firdausi Yahaya:

Ta yi fice da sunan Ma’u a shirin Garwashi, sabuwar jaruma Firdausi Yahaya tana ɗaya daga cikin jaruman da suka shigo ciki Kannywood da ƙafar dama. Domin kuwa damar da ta samu na fitowa a matsayin Ma’u a cikin shirin ‘Garwashi’ ya ba ta damar zama babbar jarumar da ta yi fice a wannan shekarar.

4. Shamsuddeen Idris:

Ya yi fice da sunan Kofor Audu a shirin Dadin Kowa. Ya kasance jarumin da yake da tasiri a cikin jaruman da suka yi fice a wannan shekarar, musamman idan aka duba rawar da ya taka a cikin shirin ‘Dadin Kowa’ a matsayi sa na Kofur Audu.

5. Usman Mu’azu: 

Tsohon furodusa ne da a yanzu ya rikiɗe ya koma matsayin jarumi, inda ya fito a ‘Gidan Sarauta’ da kuma ‘Labarina’, matakin jarumin barkwanci da ya taka a cikin fim ɗin ‘Labarina’, wato Rangila, ya fito da shi a matsayin jarumi a wannan shekarar.

6. Hafsat Muhammad:

Ta fito a matsayin ‘YarBaba a cikin shirin Garwashi. Yarinya ce da ta ƙware a cikin iya rol na ‘yammata karuwan gida, wadda ita ma a wannan shekarar ta zama fitacciyar jarumar da ta ɗauki hankalin masu kallo.

7. Fa’iza Muhammad:

Ana kiran ta da Bilkisu matar Kofor Audu, saboda rawar da ta taka a shirin Daɗin Kowa. Ta kasance jarumar da ta yi fice a wannan shekarar musamman idan aka duba rawar da ta taka a cikin shirin ‘Dadin Kowa’ da sauran finafinai masu dogon zango.

8. Abubakar Bado:

A can baya ya taka rawa sosai a cikin shirin ‘Labarina’. Musamman idan aka duba alaƙar su da Baba ɗan Audu. Amma a wannan shekarar idan aka duba rawar da ya taka a cikin shirin ‘Garwashi’, za a ga cewar a yanzu ne ma yake sharafin sa, don haka ne ya zama cikin fitattun jaruman wannan shekarar.

9. Bashir Bala Ciroki:

Masu kallon fim a wannan shekarar za su daɗe suna tuna Jarumi Bashir Bala Ciroki, domin ya fito a finafinai da yawa a wannan shekarar, amma rol ɗin da ya taka a cikin fim ɗin ‘Gidan Sarauta’, ya kai shi ga matsayin fitaccen jarumin wannan shekarar.

10. Jamila Umar Nagudu: 

Ta kasance jarumar da tauraruwar ta ba ta kwanciya a duk tsawon shekarun da ta yi tun daga fara tashen ta, saboda ta kan saje da duk wani rol da aka ɗora ta. Ita ma a wannan shekarar ta ƙara yin fice a cikin fim ɗin ‘Manyan Mata’.

11. Mommy Gombe:

Ita ma tana cikin fitattun Jaruman Kannywood da suka yi fice a wannan shekarar, musamman idan aka duba rawar da ta taka a cikin fim ɗin ‘Manyan Mata’ da Gidan Sarauta.

12. Rahama Sidi Ali:

Ita jaruma ce da tauraruwar ta ta haska a cikin fim ɗin ‘Labarina’, hakan ya kai ta ga sahun manya jarumai da suka yi fice a wannan shekarar.

13. A’isha Najamu:

Duk da tauraruwar ta a baya ta ɗan kwanta saboda tsayawar fim ɗin ‘Izzar So’. Amma dai a wannan shekarar ta yi wa masu kallo ba zata. Domin rawar da ta taka a cikin fim ɗin ‘Gidan Sarauta’, da kuma ‘Allura Cikin Ruwa’, ya mayar da ita fitacciyar jaruma a cikin wannan shekarar.