DSS ta kama wani babban jagoran Ansaru da ake zargin yana da alaƙa da Boko Haram — Rahoto

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Nijeriya (DSS) ta kama Khalid Albarnawi, wani fitaccen jagoran ƙungiyar Ansaru da ake zargin ta sake ƙulla alaƙa da Boko Haram.

A cewar rahoton, an kama Albarnawi ne a Lokoja, Jihar Kogi, kafin daga bisani a mayar da shi wani wuri a ranar Juma’a. Rahoton ya samo asali ne daga wani masani kan harkokin Boko Haram, Ahmad Salkida, wanda ya wallafa bayanin a shafinsa na ɗ.

Rahotanni sun bayyana Albarnawi a matsayin ɗaya daga cikin manyan shugabannin ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya a Nijeriya, inda masana harkokin tsaro ke kallonsa a matsayin mutum mai muhimmanci irin marigayi shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau.

An kuma ce yana da alaƙa da wasu ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi da ke Arewacin Afirka da Gabas ta Tsakiya, tare da zargin cewa ya taka rawa wajen sasanta alaƙa tsakanin wasu shugabannin Ansaru da ISWAP.

Salkida ya bayyana kamen a matsayin ɗaya daga cikin manyan nasarorin da hukumomin tsaron Nijeriya suka samu a yayin da suke yi da ta’addanci.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Hukumar DSS da Gwamnatin Tarayya ba su fitar da wata sanarwa a hukumance da ke tabbatar ko musanta rahoton ba, domin jami’an da aka tuntuɓa sun ƙi yin tsokaci kan lamarin.

By ukarofi

Leave a Reply