Dukkan sassan duniya sun tabbatar da nasarorin da aka samu a wasannin Olympics na nakasassu na lokacin sanyi na Beijing

Daga CMG HAUSA

Kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta nakasassu na ƙasa da ƙasa ya gudanar da taron manema labarai a jiya Asabar, a babbar cibiyar watsa labarai ta wasannin Olympics ta nakasassu na lokacin sanyi na birnin Beijing.

Inda shugaban kwamitin Andrew Parsons ya bayyana cewa, kwamitin shirya wasannin Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing ya gudanar da ayyuka masu ban mamaki, kuma sassa daban-daban sun tabbatar da nasarorin da aka samu a gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta lokacin sanyi ta Beijing.

Parsons ya ƙara da cewa, ’yan wasa, da tawagogin wasannin nakasassu na lokacin sanyi, da ƙungiyoyin kasa da kasa na gasanni daban daban, da hukumomin watsa labaru, duk sun ba da ra’ayin cewa, aikin kwamitin shirya wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing ya yi kyau ƙwarai da gaske, ya kuma godewa kwamitin shirya gasar a bisa namijin ƙoƙarin da ya yi kan shirye-shiryen wasannin Olympics ta nakasassu na lokacin sanyi cikin shekaru 7 da suka gabata, yana mai cewa, an cimma burin da ake buƙata kan shirye-shiryen gasar, yayin da aka kafa wani babban ma’auni ga birnin da zai karɓi banƙuncin gasar a nan gaba.

Ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta lokacin sanyi ta Beijing ta samu gagarumin ci gaba a tarihi. (Mai

Fassarawa: Bilkisu Xin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *