Har yau ban cimma nasarar da na ke fatan samu a rubutu ba – Auntyn KD

“ƙungiyoyin marubuta na taka rawa kan dawo da martabar rubutu”

Ɗaya daga cikin iyaye kuma gatan littafan adabin Kano, Sadiya Muhammad Abdullahi, wadda aka fi sani da Auntyn Kd, ta kasance jajirtacciyar marubuciya da ke kishin rubutun Hausa, hakan ta sa ta zare damtse wurin ganin ba a bar harkar ta su ta rubutu a baya ba, ta hanyar kafa ƙungiyoyi, zuwa taruka da kuma shiga hanyar fafutukar neman mafita ga marubuta. Shafin adabi na wannan sati, ya lalubo wa masu karatu ita, don haka idan kun shirya, ku biyo mu, don jin yadda tattaunawar ta kasance:

Daga AISHA ASAS

Shin wacce ce Auntyn KD?
To, ita dai Auntyn KD ba kowa ba ce, face baiwar Allah da ke neman taimakonsa a dukkan lamurranta. Da farko, cikakken sunana, Sadiya Muhammed Abdullahi. Sai dai an fi sani na da Aunty Sadiya Kaduna, wasu kuma su ce Auntyn KD. Waɗannan sunayen, albarkacin rubutu na same su. Ni haifaffiyar Kaduna ce, a Tudun Wada, Musawa road. Na yi firamare a nan Tudun Wata. Na yi ‘secondary’ a Memuna Gwarzo. A yanzu haka Ina da aure da yara bakwai. Alhamdu lillah.

Wacce shekara kika fara rubutu?
Na fara rubutu a 2007, na fitar da shi a 2008.

Zuwa yanzu kin rubuta littafai nawa?
Izuwa yanzu, na rubuta littafai guda goma.

Ko akwai ƙungiyar da kike ciki ta haɓaka harkar rubutu?
ƙungiyoyi kai akwai, domin ai duk inda ka ga ƙungiya ta marubuta, to fa gatan marubuci ce, kuma hanya ce ta sa ma masa mafita, ƙwarewa da kuma cigaba a tafiyar ta sa. Don haka ina ciki, wasu daga cikinsu; Mace Mutum da Mikiya Hausa writers.

Kenan ƙungiyoyin marubuta na taka rawa mai yawa a harkar rubutu?
Tabbas ƙungiyoyin marubuta suna taka muhimmiyar rawa akan dawo da martabar rubutu, musamman ma da yanzu abubuwa suka taɓarɓare fiye da da, suna ƙoƙarin ganin sun tsaftace rubutu, an samu rubutu mai inganci, ta yadda duk inda mai nazari ya duba, zai gamsu da ingancin shi ainihin rubutun, ba tare da ya sha wahala ba, sannan kuma, suna ƙoƙari wajen inganta rayuwar shi kansa marubucin na ganin bai zama koma-baya ba, inna ce koma-baya, Ina nufin ko yaushe a saka wa marubuci karsashin son rubutun.

Wasu na cewa, cikin dalilan da ya sa kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu a tafiyar ƙungiyoyin marubuta saboda mata ne suka fi jagoranci a cikinsu. Ko akwai gaskiya a wannan zancen?
A’a ba haka ba ne. Akwai ƙungiyoyi da dama waɗanda ba mata ba ne suke jagorantarsu, sannan kuma akwai waɗanda matan ne suke jagorantarsu, ya dai danganta ga waɗanda suke ciki akan samun ƙungiyoyin. waɗansu za ki ga jagororinsu jajirtattu ne, ba su da son zuciya, suna da kishin ƙungiyar ba wai suna suka fito yi ba, bil haƙƙi sun fito sun kafa ta ne saboda su tallafa wajen gyaran marubuci, ya zama mai rubutu da inganci ta kowanne fuska, suna da yaƙinin ganin an samu rubutu mai inganci da tsaftace rubutun shi karan kansa.

Don haka ya danganta da yadda aka kafa ƙungiyar, sannan kuma jajirce wa na taka muhimmiyar rawa wurin samun nasarar ƙungiya ko mace ce ke jagorantar ta ko namiji, misali, za ku ga ƙungiya namiji ne ke shugabantar ta, amma ba sa rasa ƙalubale a cikinta, haka ma in macen ce. A taƙaice jagorancin mata ba shine silar rashin cigaban ƙungiya ba. Don haka ya danganta da hali da kuma kishin tafiyar.

Kasancewar kinga jiya, kuma kinga yau a harkar rubutu, me kike ganin ke kawo tasgaro a yunƙurin marubuta na ganin sun ciyar da kansu gaba?
Gaskiya akwai ababe da dama, kowanne da abinda yake kawo masa hakan, amma da yawa za ki ji ɗayan-biyu, akasari yadda komai yazama ɗan zani, rubutu sai da kuɗi masu yawa sannan za ka iya fitar da littafi, to akasarin marubuta wannan tsadar rayuwar ta shafe mu, ganin yadda ko ka yi yunƙuri kafitar da kyar, dawowar kuɗin zai zama aiki. To samun ka ƙara ɗora wa shima wannan aiki ne, sannan ga kasuwar ta ja baya an raja’a a ‘online’.

Sunanki a duniyar rubutu ya yi tambari, har ana hasashen da gidan sarauta ce harkar rubutu, da tabbas kin kasance daga cikin masu mulkinta. Shin me ya ba ki wannan darajar?
(Dariya) Jajircewa da kuma kwantar da kai, haƙuri, juriya da son ganin cigaban waɗanda mu ke tare da daraja kowa, da ba kowa girmansa yadda Allah ya ba shi.

A matsayinki ta tsohon hannu a harkar rubutu, ko akwai wani shiri da kuke yi na renon marubuta masu taso wa?
Wannan mun daɗe mu na ƙoƙarin yin sa, za kuma mu ci gaba da yi iya yin mu, insha Allahu. Burinmu shine, su ma su taso su yi abinda ya kamata. Yadda su ma za a yi koyi da su nan gaba, su kuma kasance jajirtattu su ma.

Ya alaƙarki ta ke da sauran marubuta?
To, alhamdu lillahi. Duk da dai ɗan Adam tara yake bai cika goma ba, Ina kwatantawa dai dai gwargwado, sai dai kuma wannan amsar ba ni ya kamata in amsata ba, da za a bada fili aji ta bakin abokan huɗɗa, su ne za su yi ‘judging’. Ina fatan kuma in gama da kowa lafiya, insha Allahu.

Me ya kashe kasuwar littafai?
Tattalin arzikin ƙasa tare da rashin tabbas ɗin ‘yan kasuwa.

Shin akwai wani abu da kika taɓa fuskanta da ba za ki manta da shi ba ta dalilin rubutu?
Wafatin Aminiyata Zahara’u Baba Yakasai, rahimahallahu. Mutuwarta Ina jinta sosai har bana so in tuna mutuwarta, ta kasa goge wa a cikin zuciyata. Mun shaƙu, shaƙuwa irin wacce na yi da Fatima ɗan Barno da Shamsiyya Yusuf Kaduna.

Tabbas marubuciya ce da aka yi mata shaida mai kyau. Allah ya jiƙanta.
Gaskiya ne. Amin ya Rabbi.

Wanne lokaci kika fi sha’awar rubutu?
Da daddare idan kwanyata ba ‘go slow’.

A litattafanki wanne kika fi so?
Dukka ina son su, amma zan iya cire ma ki uku; ‘Alwashi’ da ‘Waye Musabbabi’ da kuma ‘Kula da Kaya’. Sannan in akace ma ki ‘Kula da Kaya’ da ‘Azal’, anzo wajen, sannan kuma ki haɗa mani da ‘Auran ƙaddara’, wanda silata aka yi shi, wanne ne ba wanne ne ba. ke dai ki yi shuru, kowanne akwai mazauninsa a cikin zuciyata.

Ko za mu iya sanin nasarorin da kika samu?
Nasarori akwai su da dama, amma har yau ban cimma nasarar da na ke mafarkin samu ba, ina ta dai addu’a, Allah ya amsa, amin.

Akwai ƙalubale?
ƙalubale kam ai ita a rayuwa ana karo da ita ta kowanne fanni. Amma ko anci karo da su, nakan ɗaukesu a ƙaddarar rayuwa, ƙaddara kuwa duk Musulmi ba ya kuɓuce mata. Allah ya ba mu ikon cin jarrabawar rayuwa, Amin.

Daga ƙarshe, wacce shawara za ki aika wa ‘yan’uwanki marubuta?
Shawarar da zan ba ‘yan’uwana marubuta itace; mu zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya, duk abinda za mu yi, mu yi shi don Allah, haka in zamu bari, mu bari don Allah. Mu dinga kishin junan mu. Ban da wariyar jinsi, mu ji, mu ƙi ji, mu gani, mu ƙi gani. Mu yi dogaro da ikon Allah. Mu dinga rubutun da zai zama gyara a wajen al’umma, wanda ko mun mutu, baza mu yi danasanin abinda mu ka rubuta, mu ka bari ba, ma’ana rubutu mai tsafta da hasashe nagari.

Mun gode.
Ni ma na gode ƙwarai.