Shugabancin APC: Musayar yawu ta ɓarke tsakanin El-Rufai da Buni

*Buhari da gwamnoni 19 ne suka kori Buni, inji El-Rufai
*Da kaina na sauka don zuwa Dubai neman lafiya, cewar Buni
*Babban Taron APC ba gudu ba ja da baya – Gwamna Sani Bello

Daga SANI AHMAD GIWA da MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Rikicin da ya ɓarke a jam’iyyar APC ya ɗauki sabon salo yayin da Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa, shugaba Buhari ya kori Gwamna Mai Mala Buni daga shugabancin jam’iyya, inda daga baya Mai Mala Buni ya fitar da wata wasiƙa da ke nuna kalaman Gwamna Nasir El-Rufa’I ba daidai ba ne.

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce, Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ya yi sallama da shugabancin Jam’iyyar APC kuma babu abin da zai sake dawo da shi kan kujerar.

El-Rufai ya zargi Mai Mala Buni da shirin hana jam’iyyar gudanar da babban taronta na ƙasa, inda ya je ya karvo umarnin kotu da zai hana gudanar da taron ya kuma ɓoye shi.

A lokacin da ya ke tsokaci kan rikicin shugabanci da jam’iyyar ta tsunduma, El-Rufai ya ce, Buni wanda yanzu haka ba ya Nijeriya zai dawo ƙasar ne kawai a matsayin Gwamnan Yobe amma ba Shugaban Riƙo na Jam’iyyar APC ba.

Gwamnan ya ƙara da cewa, bakin alƙalami ya riga ya bushe domin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari tare da gwamnoni 19 sun amince da tsige Buni daga matsayinsa, kuma yanzu haka Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello, ya maye gurbinsa a matsayin sabon Shugaban Riƙon APC.
El-Rufai ya ce, babu tantama Shugaba Buhari ne ya ba da umurnin tsige Buni, kuma an aiwatar da umarnin saɓanin raɗe-raɗin da jama’a ke yi.

Gwamnan ya ci gaba da cewa, bayan karvar jagorancin jam’iyyar da Bello ya yi, al’amura sun fara daidaita, kuma za su dawo da martabar jam’iyyar wajen gudanar da taron ƙasa kamar yadda aka shirya.

Da ma dai APC mai mulki na fama da rikicin cikin gida, inda ta sha ɗage lokacin gudanar da babban taronta na ƙasa, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.
A wani labari kuma daban, Gwamna Mai Mala Buni ya ƙaryata kalaman Gwamna Nasir El-Rufa’i a cikin wata wasiƙa da ya fitar a jiya, Alhamis. Wasiƙar ta ƙaryata jawabin El-Rufa’i na cewa, Shugaba Buhari ya bada umurnin tunɓuke Buni.

Hadiman Mai Mala sun bayyana cewa, maigidansu ba korar sa aka yi ba, da kansa ya miqa mulkin jami’yyar hannun Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, kafin tafiya jinya ƙasar Dubai.

Wani sashen wasiƙar mai ɗauke da kwanan watan 28 ga Febrairu ta ce, “Ina mai sanar da kai cewa zan tafi neman lafiya Ƙasar Daular Larabawa (Dubai) daga yau, 28 ga Febrairu, 2022.”

“Saboda haka, na wakilta ayyukan ofishina na Shugaban Kwamitin Riƙon Qwaryar Jam’iyyar nan gare ka. Ina kira ga mambobi su haɗa kai da Gwamna Abubakar Sani Bello ta hanyar ba shi goyon baya kamar yadda kuka bani.”

Wani hadimin Buni, wanda ya buƙaci a sakaye sunansa ya bayyana wa manema labarai cewa, “ba zai yiwu a ce wani ko gungun gwamnoni sun cire Buni ba, saboda wasiƙarsa a bayyana ta ke. Ya bi ƙa’ida kuma ya ce Bello ya wakilce shi.

“Ya kamata Gwamna El-Rufa’i ya faɗa wa Nijeriya gaskiyar abinda ya afku tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da wasu gwamnoni ranar Lahadi. Akwai kura-kurai cikin maganarsa. ’Yan Nijeriya su tambayi Bello da mambobin kwamitin riƙon ƙwarya ko Buni ya ba su wasiƙa ko akasin haka.”

A wani cigaban kuwa, Kamfanin Dillacin Labarai na Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa Gwamnan Jihar Neja, kuma sabon Shugaban Kwamitin Riƙo na Babban Zaɓen Jam’iyyar APC na Ƙasa (CECPC), ya bayyana cewa babban zaɓen shugabannin jam’iyya da za a gudanar a matakin ƙasa, ranar 26 ga watan Maris 2022, babu gudu ba ja da baya, kuma ba zai zo da wata tangarɗa ba.  

“Ranar babban taron jam’iyyar mu kamar yadda aka tsara yana nan daram, tilas ne mu yi shi 26 ga Maris, kuma za mu yi duk mai yiwuwa don ganin an gudanar da shi. Kamar yadda wasun ku suke kula da duk abubuwan da muke yi a sakatariyar jam’iyyar tun ranar Litinin, mun fara ƙoƙarin ganin mun gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci.

“Muna ƙoƙarin ganin mun yi nasarar tabbatar da babban taron mu, wanda yana ɗaya daga cikin ƙoƙarin da muka yi na rantsar da shugabanni da sakatarorin kwamitin shirya babban taron,” inji shi.

Gwamna Sani Bello da yake kira ga ‘yan kwamitin shirya zaɓen, ya hore su da au kasance masu gaskiya da riƙon amana don ganin an samu gagarumar nasarar gudanar da babban taron, inda ya ce an zaɓe su ne saboda kasancewar su masu biyayya ga jam’iyya.

Bello ya kuma shaida cewa kowane yanki a faɗin ƙasar zai samu wakilci daga cikin ‘yan kwamitin, wanda yana daga cikin manufofin  jam’iyyar APC na ganin ana yi da kowane ɓangare.

Ya kuma jinjina wa mambobin kwamitin shiryar babban taron jam’iyyar (CECPC) wajen cigaban da aka samu. Gwamnan Jihar Ekiti, Fayemi Kayode wanda ya yi magana da yawun mambobin kwamitin, ya gode wa shugabancin jam’iyyar da ya ba su damar bayar da gudunmuwar su wajen cigaba da bunƙasar jam’iyya. Ya kuma bada tabnacin mambobin kwamitin za su gudanar da ayyukan su ka-in-da-na-in don ganin an samu nasarar gudanar da taron.

“Muna son mu gode wa jam’iyyar mu mai farin jini da ta ba mu wannan dama don bayar da gudunmuwar mu wajen cigaban ta da bunƙasarta. Wannan aiki ne da yawanci suke jira da daɗewa,” a cewar sa, mambobin kwamitin za su jajurce kuma su bada himma wajen gudanar da ayyukan da aka ɗora musu don cimma muradun jam’iyyar su ta APC da kuma mambobinta

Fayemi ya jinjina wa Gwamna Sani Bello da kuma mambobin kwamitin shirya babban taron (CECPC) akan aikin su na ƙara ƙarfafa jam’iyya, inda ya ce “mun shirya tsaf wajen sadaukar da kawunan mu a madadin sauran ‘yan kwamitin.” 

Ranar Labara ne jam’iyyar APC mai mulki ta yi gyara a kwamitin zaɓen shugabanninta na ƙasa. An samu wannan sauyi ne bayan gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya karvi riƙon jam’iyyar daga hannun Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, inda ‘ya’yan jam’iyyar da wasu gwamnonin APC suka yi ƙorafin Mala Buni ya zuba mutane kusan 1,200 a cikin ‘yan ƙananan kwamitocin da za su yi aikin zaɓen shugabanni na ƙasa da aka tsara za a yi a ƙarshen Maris.

Sabon shugaban kwamitin riƙon ƙwaryan na APC, Abubakar Sani Bello ya ce mutanen da Buni ya lafta sun yi yawa a wajen gudanar da zaɓen shugabanni.

A halin yanzu rahotanni sun nuna an zaɓi mutane 107 ne kaɗai su yi wannan aikin. A haka ba a haɗa da waɗanda suke cikin babban kwamitin gudanarwa ba kamar yadda rahoton ya nuna.

A wannan sauyi da Sani Bello ya kawo a makon nan, Maigirma Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar aka zaɓa ya jagoranci aikin.

Da yake rantsar da ‘yan kwamitin na Gwamna Badaru Abubakar, Abubakar Sani Bello ya ce APC ba za ta iya jibga mutane da yawa a kwamitin zaɓen na ta ba.

Amma duk da haka Bello ya ce akwai buƙatar a tafi da kowa a cikin ƙananun kwamitocin, inda ya ce ragin da aka yi bai nufin an raina wasu ‘yan jam’iyyar.

Haka zalika rahoton ya cigaba da cewa canjin da sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa ya kawo, ya na nufin an cire mutane 893 daga aikin shirya zaɓen da za a yi.

“Mun rage yawansu zuwa adadin da za su yi iya aiki, ba tare da raina kowa ba, kuma ina tunanin wannan ya fi dacewa da jam’iyyar mu,” inji Gwamna Bello.

Za a ga kusan duka qananun kwamitocin suna ɗauke ne da mutane huɗu. Bayan shugaba wanda ake zaɓan wani babba a gwamnati, sai sakatare da mutane biyu.

Idan ba a manta ba tun ranar Litinin jam’iyyar APC ta kasance cikin ruɗani, inda aka hangi Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya jagoranci rantsar da mambobin kwamitin shirya babban taron jam’iyyar.

Hakan ya sa aka shiga tababar an yi wa Gwamna Mai Mala Buni wanda shi ne Shugaban Riƙon Ƙwarya na jam’iyyar juyin mulki, inda wasu rahotanni suke bayyana cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne da kansa ya bada umarnin a tunvuke shi, a daidai lokacin da wasu gwamnoni ke zargin Buni da aniyar ƙin gudanar da babban zaɓen da jam’iyyar ke son yi a ƙarshen watan Maris ɗin nan.

Sai dai har zuwa haɗa wannan rahoto, Fadar Shugaban Ƙasa ba ta fito ta bayyana komai ba akan wannan saka-toka-sa-katsin, amma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufai a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channel, ya bayyana cewa Shugaba Buhari ne da kansa ya bada umarnin a tsige Mai Mala Buni a kan shugabancin jam’iyyar.

Wannan dambarwa dai ta sa masu fashin baƙi kan lamuran siyasa sun ta tofa albarkacin bakin su, inda suke ganin cewar jam’iyyar ta APC za ta iya fuskantar babbar baraza duba da yadda kawunan gwamnonin APCn ke a rarrabe, a cewarsu.