Sanata ya tallafa wa makarantar marayu a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

A cikin shirinsa na tallafa wa marasa galihu Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi Mallamawan Kabi mai wakiltar gundumar Kebbi ta Arewa kuma shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa ya tallafa wa makarantar marayu da ke ƙarƙashin kulawar ‘Mar’atussaliha’ ƙungiyar nan ta mata mai rajin kare mutuncin zawarawa da marayu da ke garin Argungu a jihar Kebbi da kayan aiki.

Da ya ke jawabi lokacin miƙa kayan shugaban kwamitin gudanarwa na siyasar sanatan, Alhaji Aliyu Gandu Augie ya bayyana cewa wannan aikin ba sabon ba ne ga duk ɗan wannan yankin saboda kamar yadda kowa ya sani babu ɓangaren da aikin Sanata Dr. Yahaya Abubakar bai kai ba illa dai abinda ya rage yanzu shi ne ke bin mutanen mazaɓarsa ba shi.

Ya  yi kira ga hukumar makarantar da kuma shugabannin gudanarwa na wannan ƙungiyar da su yi amfani da waɗannan kayan ta yadda ya kamata, kada su yi son rai saboda ko ba komai dai waɗannan kayan marayu ne.

Ya kuma ƙara da cewa ala kulli halin ƙofar Sanata Dr. Yahaya Abubakar Abdullahi a buɗe ta ke don sauraren buƙatun al’umma musamman ta hanyar mataimakan sa.

Hajiya Mariya Muhammadu Mera ita ce shugabar wannan ƙungiyar ta Mar’atussaliha ta yi godiya ga Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi bisa ga wannan karimcin da kuma irin ƙoƙarin da ya ke yi a zauren majalisar dattawa. Ta bayar da tabbacin yin amfani da waɗannan kayan ta yadda ya kamata.

Hajiya Mariya ta bayyana cewa yau kimanin shekaru biyu kenan da kafa wannan ƙungiyar amma da taimako maau hannu cikin ikon Allah ta ɗauki nauyin sama da marayu dubu biyu wajen dinka musu tufafi a lokutan Sallah, ta kuma dauki nauyin kai su wajen koyon sana’o’i dabam-daban kama daga koyon ɗinki, kayan man shafi aikin kafinta da dai sauransu.

Hajiya Mera ta ƙara da cewa duk da ya ke wannan ƙungiyar ta yi ta yunkurin saduwa da Sanata Allah bai ƙaddara ba amma dai suna da tabbacin ƙungiyar tana ran sa saboda ya sha tallafawa musamman a lokutan azumi saboda haka ƙungiyar tana godiya, har wa yau dai kuma tana miƙa ƙoƙon baran ta na neman ƙarin gine-gine da samar da ruwan sha da kuma lantarki mai aiki da hasken rana da kuma kekunan ɗinki don inganta koyon sana’o’in su.

Kayan dai sun haɗa katifu da filalla da zannuwan gado da manyan tukwanen dafa abinci da kujeru da tebura na malamai da ɗalibai da kuma kayan rubutu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *