Fashewar tukunyar gas ta jikkata mutane biyar da ƙona gidaje da shaguna 17 a Jigawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Aƙalla mutane biyar ne su ka ji raunuka daban-daban’, yayin da gidajen mutane da shaguna suka qone biyo bayan fashewar wata tukunyar gas a Ƙaramar Hukumar Babura, jihar Jigawa.

Kakakin rundunar tsaron Sibil Defence (NSCDC) reshen jihar Jigawa, Adamu Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar da safiyar Talata.

Ya ce lamarin ya faru ne lokacin da wata babbar motar dakon kaya maƙare da tukunyar gas ta yi bindiga a garin Babura.

Kakakin NSCDC ya ce gidaje da yawa da shagunan al’umma sun ƙone sakamakon faruwar lamarin, inda ya ƙara da cewa mutane da dama sun jikkata, amma har yanzu babu wanda ya mutu.

“Mummunan lamarin ya auku ne da daddare, ranar Litinin 12 ga watan Satumba, 2022 da misalin ƙarfe 9:00 na dare,” inji shi.