Daga CMG HAUSA
Yawan fasinjojin da suka tashi da ma sauka a filin jirgin sama na Beijing Daxing na ƙasar Sin, ya zarce miliyan 52 a cikin shekaru 3 da suka gabata.
Bayanai na nuna cewa, a cikin shekaru uku da suka gabata, filin jiragen saman na Daxing, ya kula da tan 370,000 na kaya da wasiku.
Kuma jirage 450,000 ne suka tashi ko kuma suka sauka a filin jirgin.
A halin yanzu, kamfanonin jiragen sama 26 na cikin gida ne suke aiki a filin jirgin saman. Haka kuma filin jirgin saman, ya buɗe jimillar hanyoyin jiragen sama guda 266, tare da hada sassa 185.
A jiya ne dai, aka yi bikin cika shekaru uku da fara ayyuka a filin jirgin saman na Daxing.
Mai fassara: Ibrahim Yaya
