Ƙasar Amurka ce kan gaba wajen yaɗa labarai marasa tushe

Daga CMG HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin ya yi tsokaci game da rahoton da ofishin sa ido kan yanar gizo na jami’ar Stanford ta ƙasar Amurka ya gabatar, inda ya ce, cikin shekaru da dama da suka gabata, ƙasar Amurka ta kafa tsarin faɗakarwa mai girma ta kafafen sada zumunta game da ƙasashen Sin, da Rasha, da Iran da sauransu, don yaɗa labarai marasa tushe da faɗakar da harkokin siyasa ta hanyoyin buɗe shafukan jabu, da yaɗa labarai kusan iri ɗaya, domin jan hankalin mutane.

Kakakin ya ƙara da cewa, Amurka ce babbar mai yaɗa labaran ƙarya, amma tana ci gaba da ɗaura laifi da ɓata sunan wasu ƙasashe.

Ya ce a bayyane yake cewa, Amurka ta buɗe shafukan jabu da yawa, amma ta sa kaimi ga kafafen sada zumunta su rufe shafunan jama’ar Sin.

Haƙiƙa Amurka ce mai yin tasiri kan ra’ayoyin jama’a, amma kuma ta mayar da dukkan kafofin watsa labaru na Sin a matsayin shafunan gwamnatin ƙasar.

Ƙasar Amurka na shafa wa ƙasar Sin baƙin fenti, amma kuma sai take zargin ƙasar Sin ɗin da yada ra’ayin kin Amurka.

Mai fassara: Zainab