Masanan Amurka: Cutar COVID-19 ba ta ƙare ba tukuna

Daga CMG HAUSA

Yayin da ake mayar da martani game da maganar cewa, “Cutar COVID-19 ta riga ta ƙare a cikin Amurka”, kwanan nan wasu masana a Amurka suka fitar da wani bayani dake nuna cewa, ba a shawo kan cutar ba tukuna a cikin ƙasar, kuma ganganci ne da rashin hankali a riƙa wasa da annobar.

A kwanakin nan ita ma jaridar Washington Post, ta wallafa wani sharhi, inda ta jaddada cewa, cutar COVID-19 ba ta ƙare ba a Amurka.

A cikin bayanin, an ce cutar COVID-19 ta daɗe tana yaɗuwa, inda wasu mutane suka mutu sanadiyar kamuwa da ƙwayar cutar, kuma cutar tana ci gaba da sauyawa, tare da mamaye duniya.

A cewar sabon rahoton mako-mako game da cutar COVID-19 da cibiyar kandagarki da hana yaɗuwar cututtuka ta Amurka ta fitar, ya zuwa yanzu, matsakaicin mutane dubu 60 ne suke kamuwa da cutar a kowace rana, kuma matsakaicin ƙaruwar mutanen da suka mutu sanadiyar cutar a kwana guda, sun kai 358.

Ban da wannan kuma, tun lokacin da cutar COVID-19 ta ɓarke a cikin Amurka, mutane fiye da miliyan 95 ne aka tabbatar sun kamu da cutar, yayin da cutar ta halaka mutane fiye da miliyan 1.

Mai fassarawa: Safiyah Ma