Gwamnati ta janye umarninta kan jami’o’i su koma bakin aiki

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, ta janye umarnin da ta bayar kan hukumomin jami’o’in gwamnatin kasar nan da ke yajin aiki su koma bakin aiki.

Gwamnatin ta janye umarnin nata ne ta hannun Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC).

Za a iya tuna cewa tun farko an rawaito gwamnatin, cikin wata wasiƙa da Daraktan Kuɗi na hukumar NUC, Sam Onazi, ya sanya wa hannu a madadin Sakataren hukumar Farfesa Abubakar Rasheed, ta ba da umarnin shugabannin jami’o’i su buɗe makarantu sannan a bai wa ɗalibai damar komawa aji.

“A tabbatar da mambobin ASUU sun koma bakin aiki nan take, a kuma maido da harkokin jami’o’i kamar yadda suke,” inji wasiƙar.

Kwatsam, sai aka sake ganin wata sanarwa daga hukumar NUC mai lamba:
NUC/ES/138/Vol.64/136, kan janye umarnin sake buɗe jami’o’in da gwamnati ta bayar da farko.

Sanarwar mai ɗauke da kwanan wata 23 ga Satumba 2022, ba ta fayyace dalilin da ya sa gwamnatin janye umarnin nata ba.

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da Kotun Ma’aikata ta bai wa ASUU umarnin janye yajin yakin da take yi ba tare da bata lokaci ba, lamarin da ita ASUU ta ce ba ta ga ta zama ba za ta haɗa kan manyan lauyoyi domin ɗaukaka ƙara.