Makaɗin Hausa: Salihu Jankiɗi (1852-1973)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An haifi Salihu Jankiɗi ne a garin Rawayya ta ƙasar Bungudu ne a yanzu cikin ƙaramar Hukumar Gusau, wajejen shekara ta 1852. Sunan mahaifinsa Alhassan ɗan Giye ɗan Tigari mai abin kiɗi. Salihu shi ne sunansa na yanka, amma kanen uwarsa Kardau ya yi masa laƙabi na Jankiɗi saboda jan da Allah ya ba shi wanda ya bi shi har bayan rasuwarsa.

Alhassan Giye Ɗan Tigari:

Mahaifin Jankidi Alhassan Makadi ne na kalangu kuma mai yawan yawace-yawace don kiɗa. Yakan bar garinsu Rawayya ya shiga uwa duniya don sana’arsa ta kiɗa. Shi kuma makaɗi ne na lokacin kiɗan yaƙi. Ya je Argungu da Bida da Kwantagora da Kotonkoro da sauransu, amma yana komawa gida Rawayya. Daga baya ya tashi zuwa Kotonkoro, sai kuma ya tare Kwantagora wurin sarkin Sudan Ibrahim. Ya yi masa wakoki da yawa, amma wadda ake iya tunawa ita Ce:

Namiji kamar maza ya kai.
Jikan Shehu na tsaye.
Na Garba waiwaya bayanka.
Ka hi damben juya da kahirai.

Ƙuruciyarsa da tasowarsa:

Salihu Jankiɗi ya buɗe idonsa a Kwantagora a nan ne ya yi rayuwarsa ta ƙuruciya. Ya tashi yana yaro mai ƙarfi da kurari, da kwarjini a tsakanin jama’a, sannan ja ne kamar tsada, tsaka-tsaki ne a wajen ƙirar jikinsa dangane da tsawo da baga. Jankiɗi ya yi dambe da kokawa da sauran wasu ayyukan samartaka na sha’awa. Saboda kasancewar Salihu ya tashi cikin yaƙe-yaƙe kafin zuwan Turawan Mulkin Mallaka duk kusan abubuwan da ya yi na yarinta na nuna ƙarfi da bajinta ne. Ya yi karatun allo inda har ya sauke Alƙur’ani mai tsarki ya kuma karanta wasu daga cikin ƙananan littattafan addinin Musulunci kamar Ƙawa’idi da Ishmawi da Kurɗabi da sauransu. Amma fa bai yi ilimin addini na littattafai mai zurfi ba.

Koyo da fara waƙoƙinsa:

Makaɗi Alhassan shi ne ya fara koya masa kiɗa da waka inda ya soma bin sa kiɗa har ya fara kaɗa kuntakuru watau kanzagi. Daga nan kuma ya shiga cikin ’ya’yensa mata masu amshi. Lokacin masu yi wa mahaifin nasa amshi, su ne:

-Umma Tsohuwa

  • A’ishatu
  • Halimatu Bakabai
  • Salihu Jankiɗi — daga baya ya soma. Haka kuma mahaifinsa Alhassan ya taba ba da shi riqo ga ɗan uwansa makaɗa ɗan Yawuri don ya koyi kiɗan kalangu sosai da sosai,

Bayan rasuwar Alhassan, sai Salihu Jankiɗi ya ɗauki shugabancin kida a nan Kwantagora tare da waɗannan mataimaka:

  • Alhajiya — ’Yar Halimatu Bakaba
  • A’ishatu
  • Halimatu Bakaba

Koyo da fara waƙoƙinsa:

A lokacin da ya fara kiɗan, sai ya haɗa kiɗan noma da kiɗan fawa a lokaci guda yana ta yi duk wanda ya samu a yi. Kuma da dai kalangu gadon gidansu ya ke wannan nau’in kiɗa. Daga cikin yaƙi da ya yi na farko-farko, akwai wannan:

Yo gaba dai salsalon nibatau,
Sanda mazan burdumi da galma.
Mai son noma da dan magaji,
Sai shi bido sulkuna da gari,
Don a yi kwanan wata gudane

Bayan da Turawan mulkin mallaka suka fara yaƙe-yaƙensu da ƙasashen Hausa har lokacin da suka zo ita Kwantagora suka yi yaki da ita, sai Kwantagora ta fashe.

A wannan halin ne Salihu Jankiɗi da sauran iyalinsa suka koma Kotonkoro. Daga nan sai Bagega cikin ƙasar Talatar Mafara, sai zuwa Kanoma, sai Bungudu, sai ya sake komawa Kwantagora bayan ƙare yaƙi.

Daga nan kuma sai Salihu Jankiɗi ya koma gida Rawayya. Da yaƙi da Turawa ya ƙare, watau sun kama dukkan ƙasashen Nijeriya sosai, suka kuma shimfida mulki irin nasu wanda suke buƙata, sai sarakunan da Turawan suka tabbatar (sababbi da tsoffi) suka ci gaba da mulkin ƙasashensu. Daga wannan lokaci ne fa Salihu ya Jefar da kalangu ya kama taushi (tafashe) gadan-gadan yana yi wa sarakuna waƙoƙi.

To, sai daga Rawayya ya koma Tsahe wurin ’Yandoto Muhammadu (1897—1924) da ’Yandoto Ibrahim Maikano (1926—1928) ya yi musu waƙoƙi. Sai kuma Salihu Jankidi ya kwashe iyalinsa ya koma Gusau da zama wajen sarkin Katsinan Gusau Muhammadu Mai’akwai (1929—1943).

Daga Gusau Salihu Jankiɗi bai koma cirawa zuwa wani wuri da nufm ya zauna ba, sai dai ya je ya kai kiɗa ya dawo Gusau ɗin. A cikin wata waƙa da ya yi wa Sarkin Katsinan Gusau Muhammadu Mai’akwai yana cewa:

Ni Jankiɗi ba ni zuwa ko’ina,
Kwadai na ba shi wucewar Gusau.
Lalle ba mu zuwa ko’ina
Kwadai na ba shi zuwa ko’ina

Bayan da aka fitar da sarkin Katsinan Gusau Muhammadu Mai akwai aka naɗa Shehu ɗan Sama’iIa sarkin Kudu (1943—1945), sai Jankidi ya koma wurin Sarkin Musulmi Abubakar III (1938—1988) ya zama ubangidansa.

Suna zaune tare da sarkin Musulmi har zuwa lokacin da ya naɗa shi sarkin taushinsa. A wajen naɗin nasa an yi gagarumin biki inda makaɗa yan’uwansa suka haɗu, aka yi masa tattaki, magaji mai farai shi ne ma ya yi busar naɗin don sheda wa jama’a.

A cikin wata waka da ya yi wa sarkin Musulmi, Salihu Jankiɗi ya yi godiya ainun. Yana cewa:

Godiya mu kai wa sarkin Musulmi,
Da yai ma sarkin taushi,
Yau batun Allah ya tabbata,
Babu sauran mai wata gardama.

(Jankiɗi: riƙa girma ka isa Bubakar)
Yaran Salihu Jankiɗi (’Yan karɓi)

’Yan karbin Jankiɗi na farko na lokacin kiɗin noma da fawa da na samartaka su ne:

  • Aishatu
  • Halimatu Bakaba
  • Muhammadu
  • Alhajiya
  • Bahago
  • Ajiya

Yan karbin Jankiɗi na faɗa:

  • Makaɗa Ibrahim danƙaro ɗansa ne
  • Mal. Abdullahi shi ma dansa ne.
  • Musa Dangaladirna Labbo: ɗansa ne.
  • MuhammaduTambai: Yaronsa ne.
  • Hassan: ɗansa ne,
  • Abduhlahi Jan Darno (Kaka): Yaronsa ne
  • Na Goje : Yaronsa ne
  • Umaru Kwairo: Yaronsa ne

Yawace-yawacensa:

Salihu Jankidi ya yawata mafi yawan ƙasashen Nijeriya, musamman ɓangaren Arewa. Ya zagaya dukkan manyan garuruwan Jihar Sakkwato da wasu ƙananan garuruwan. Haka kuma ya je Kano da Haɗejiya da Daura da Katsina da Mani da Zariya da Kaduna da Bida da Ilorin da Minna da Ibadan da Legas da Inugu kai da dai sauran ƙasashe.

Shirya waƙa:

Da farko Sahihu Jankiɗi yakan sami labarai da bayanan da ya ke sa wa a waƙa ta hanyar fadawan sarki da hira da sarakuna kansu da ta ɓangaren hakimai da masu unguwanni. Kuma yana sane da abubuwan da ya ke gani suna gudana a faɗa da kuma cikin gari.

Salihu Jankiɗi mafi yawa ya fi tsayawa gida ya shirya waƙoƙinsa, kodayake yakan yi wasu waƙoƙin nan ta ke inda duk suka samu. Amma waqar da ya tsaya gida ya tsara ita ta fi daɗi da ƙayatarwa da ƙunsar abubuwan ban sha’awa.

Rasuwarsa:

Salihu Jankiɗi ya rasu ranar Juma’a 13 ga watan Oktoba 1973 a lokacin yana da shekaru ɗari da ishirin (120) a duniya. Allah ya gafarta masa, Amin.