Daga BABANGIDA A. GORA a Katsina
A ranar Asabar ɗin makon jiya ce gidaunyar ‘Voice of the Voiceless’ wato gidauniyar da ke share wa marasa gata hawayen su, ta yi taron taimakon matan sojojin da su ka mutu suka bar iyalan su don kare martar ƙasar su da al’ummar ƙasa.
Gidauniyar wadda ke gudanar da ayyukanta a jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Hajiya Hadiza Rumah, ta kuma ba ‘yan gudun hijira tallafin kayan abinci da sauran kayan da zai rage ma su raɗaɗin rayuwa.
Hajiya Hadiza ta kuma ce wannan gidauniya ta shafe shekaru sama da goma tana gudanar da ayyukanta a jihar Katsina tare da isar da saƙon marasa gata ga gwamnati don taimaka ma su tare da ɗaukar matakan da ya dace.
Shugabar ta kuma ce sun rarraba wa matan sojojin ne kayan abinci yayin da suka ba yaran su bargunan rufa da za su yi amfani da shi don magance yanayin sanyi a halin da ake ciki yanzu na hunturu.
Sannan ta kuma ce lallai suna aiki tuƙuru ne don nemo mutanen da suke da buƙata ta musamman ba wai kawai kowa ba ne, su na ɗaukar waɗanda ba su da halin cin yau da na gobe ne don taimaka ma su.
Ta ce banwai sai ka bansu na tsawon lokaci ba ne ba, a’a mafi yawan su suna ɗaukar mafi akasarin wanda suka zo daga karkara ne don neman taimako, kama daga gudun hijira da gajiyayyun da ka gan su kansan suna da buƙatar taimakon.
Ruma ta ce, tun tsawon lokacin da suka fara tafiyar da wannan gidauniyar sun kasance ba su da yawa tare da ƙarancin abin da za su ba su mai yawa, amma duk da haka suna jaraba taimaka ma su kaɗan-kaɗan.
Hajiya ta ci gaba da cewa a lokacin da matsalar garkuwa da mutane ta kunno kai suka fara tunanin yadda za su taimaka wa waɗannan mutane da suka baro ƙauyukan su, amma kuma suka rasa ta inda za su fara, cikin yardar Allah sai hukumar hana fasa ƙwauri wato kwastam ta fiddo tallafin da za su fara badawa ta hannun su kasancewar a Katsina lokacin akwai ƙungiyoyi da yawa, amma ba su da rajista da CAC, sa’ar ita ce wannan gidauniyar ta su tana da cikakkiyar rajista.
Haka zalika ta ce lallai wannan gidauniya ta yi nasarar ƙara ba mata jari da za su ƙara dogaro da kai don taimaka wa iyalan su.
Sannan kuma ƙungiyar ta yi nasarar taimakon matan da aka yi wa fyaɗe wajen harin ‘yan ta’adda, wanda sukan ɗauko su tare da yi ma su magani daga garuruwan su.
“Haka wannan tafiya ta ƙara nasara wajen bai wa matasa jarin da za su dogara da kan su maimakon su zama cikin wani hali da kan iya jefa su cikin mugun yanayi,” inji ta.
Batun gwamnati jihar Katsina da wannan gidauniya suna aiki kafaɗa da kafaɗa, musamman lokacin da ‘yan gudun hijara suka yi yawa sun buƙaci gwamnati da ta taimaka wajen ganin an taimaka wa waɗannan mutane da satar shanu da garkuwa da mutane ta sa suka bar gidajen su, kuma kasancewar gwamnatin jihar Katsina na da fahimta komai suka buƙaci ta yi lallai takan duba yiwuwar haka tare da aikatawa.
Haka kuma Hajiya ta bayyana buƙatar taimakon wannan gidauniya wajen sama ma su ababen hawa da dai sauran abin da ba a rasa ba don gudanar da ayyukan su cikin sauƙi.
Sannan ta ƙara jinjina wa gwamnatin Jihar Katsina bisa amsa kiran su da take idan buƙatar su ta taso, haka kuma ta nuna matuƙar godiyar su ga masu riƙe da sarautun gargajiya bisa namijin ƙoƙarin su na wayar wa da al’ummar jihar Katsina kai.
Rumah ta tabbatar da cewa gidauniyar tana aiki ne iya jihar Katsina kaɗai, amma suna sa ran nan gaba idan Allah ya sa ta bunƙasa su ci gaba a sauran jihohi daga Arewa zuwa Kudu, kasancewar membobin wannnan gidauniya ma su ƙaimi ne da jajircewa wajen aiki da ƙarfin su da ma aljihun su.
Shugabar ta ce lallai ganin taimakon marayu da marasa galihu na ɗaya daga cikin abu mai kyau da yake samar da lada, sannan wasu za su iya taimakawa, ta wannan hanya ne ya qara ma su qaimi wajen kasancewar gidauniyar tana shiga lungu da saqo wajen gano ma su buqatar daban-daban tare da hanyar da za su taimaka ma su.
Kaxan daga cikin kayan da suka raba sun haxa da bargunan sanyi, shinkafa, wake da sauran kayan abinci daban-daban.
Da suke nuna godiyar su waxanda suka amfana da taimkon, iyalan matattun sojojin tare da ‘yan gudun hijara, sun nuna godiyar su ga wannan gidauniya bisa ga wannan taimakon da ba kowa ke ba su ba, haka zalika sun yi wa shugabanin wannan vangaren da ma duk wanda suka sa hannu a wannan agaji ya isa gare su.
Daga ƙarshe ta nuna matuqar godiyar ta ga sauran ma su hannu da shuni da suke sa jarin su don taimakon al’umma, tare da abokan tafiyar su a wannan gidauniya.