Mu cigaba da ɗora mabiyanmu kan turbar zaman lafiya – Sarkin Hausawan Ijede

Daga DAUDA USMAN a Legas 

Tun bayan shigowar sabuwar shekarar Miladiya ta bana waɗansu daga cikin al’ummar Nijeriya suke ta gudanar da addu’o’i na musamman domin neman izini a wajen Ubangiji Subahanahu wata Ala na ƙarin samun zaman lafiya a ƙasar nan tare da kiraye-kiraye ga sarakunan al’ummar Hausawa mazauna jihohin Kudu da yammacin Nijeriya da sauran shuwagabannin al’ummar qasar nan da su cigaba da ɗora mabiyansu a bisa kan turbar zaman lafiya.

Alhaji Muhammadu Rabiu Sale ɗan asalin ƙaramar hukumar Funtuwa ta jihar Katsina mazaunin birnin Legas kuma Sarkin al’ummar Hausawan Unguwar Ijede dake ƙaramar hukumar Ikorodu a Legas, yana ɗaya daga cikin waɗanda suka gudanar da irin waɗannan addu’o’i.

Yayin da a ranar Asabar ta ƙarshen makon nan da ya gabata Sarkin Hausawan na unguwar Ijede ya gudanar da taron addu’o’in nema wa Nijeriya ƙarin samun zaman lafiya tare da taron addu’ar sanya wa ɗansa suna wanda matarsa Rukayya ta haifa masa kuma aka sanya masa suna Adamu.

da fatan Allah ya rayashi a cikin rayuwa irin ta musulunci taron adduoin guda biyu sun gudana ne a harabar fadar sarkin hausawan na unguwar Ijede dake Ikorodu Malam Muhammadu Nasiru Sarkin Hausawan na Ijede shine ya jagoranci sauran malamai suka gabatar da addu’o’in guda biyu mahalarta taron sun haɗa da malaman Hausawa da Yarabawa da na Nufawa da sauran al’umma waɗanda suka fito daga sassa daban-daban na cikin garin Legas.

Malam Muhammadu Nasiru Limamin Hausawan na Ijede bayan sun kammala addu’o’in guda biyu ya ci gaba da jawo hankulan hausawan Ijede da na jihar Legas bakiɗaya da su cigaba da neman zaman lafiya da sauran ƙabilun da suke zaune unguwar.

Shi ma da yake gudanar da nasa tsokacin a wajen taron addu’o’in guda biyu, Sarkin Hausawan na Unguwar Ijede Alhaji Muhammadu Rabiu Sale bayan ya kammala yi wa malamai da sauran manya-manyan baƙi barka da zuwa sannan kuma ya cigaba da shawartar sarakunan al’ummar Hausawa mazauna jihohin kudu da yammacin Nijeriya da sauran shuwagabannin al’umma da sauran waɗanda suka fito daga bakunan al’umma daban-daban waɗanda suka tofa albarkacin bakinsu a wajen taron. 

Wasu Hausan Ijede

Salisu Sale ɗan’ uwan Sarkin na Ijede da M. D Hassan da Malam Sani wakilan sarkin hausawan Ikorodu da Malam Abubakar ba nu fe Ijede da Malam Muhammadu Kuda Bidda da sauran alumma wadan da suka yi tsokaci awajan taron dukkan jawabansu sun karkatane a wajan kiraye-kiraye ga sarakunan al’ummar lafiya.