
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Juma’a shahararren mai shirya fim kuma darakta, Mallam Aminu Saira ya auri mata ta biyu.
An gudanar da ɗaurin auren ne a garin Azare da ke Jihar Bauchi a wani yanayi na farin ciki da san-barka.
Taron ɗaurin auren ya haɗa mutane da dama ciki har da abokan aiki, masoya da masu ruwa da tsaki a harkar finafinai a sassan Arewacin Nijeriya, waɗanda suka taya daraktan murna bisa ƙaruwar da ya samu da kuma addu’o’i daga al’umma ta kafar Soshiyal Mediya.
Bayan ɗaurin auren, an yi ta yaɗa hotunan Aminu Saira da ya ɗauka tare da matan nasa biyu, lamarin da ya haifar da cece-kuce acikin masu amfani da dandalin sada zumunta akan auren sama da mace guda da haɗa kan iyali.
Tuni dai masu tsokaci da masoya suka riƙa jinjina wa Saira bisa bayyana lamuran rasuwarsa ta cikin gida a fili, yayin da abokan aiki a masana’antar Kannywood ke cigaba da masa fatan alheri.



