Fulani ku haɗa kanku

Ga dukkan alamu za a iya samun shawo kan wasu matsaloli da ke tattare da ƙabilu na Fulani. Mun ji sabon shugaba na Tabito Fulako wanda tsohon gwamna na jihar Bauchi ne.

Malam Isah Yuguda wanda ya zamo shugaba na dukkanin ƙasashen nafiyar Afrika. Muna fatan yan uwa fulani a taho a haɗu a zamo an maido ma jinsin kima da martaba irin ta tun farko.

Fulani mun gado kunya da kawaici da kamun kai amma a ka samu wasu waɗanda rashin ilimi da rashin tarbiyya ya rinjaye su zuwa ɗaukar hanyar ta’addanci da badala.

Muna fatan Allah ya sanya su dawo a kan hanya ta kwarai a gudu tare a tsiri tare. Kar mu manta a matakai na ɗaukaka ta addini Shuhu Usman Ɗan fodiye jinsin fulani ne.

Haka da dama almajiranshi waɗanda ya basu tutoci na shugabanci bayan jihadi. Haka a yanzu haka a majalissa ta ɗinkin duniya mai matsayi ta biyu Amina J Muhammed na daga fulani wanda hakan ke fiddo kimar Fulani a dukkanin fannoni. Allah ka sanya aminci ya dawo.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina. 07066434519\08080140820.